logo

HAUSA

Me ya sa mahalarta CAEXPO a bana ke sha’awar sake halartar bikin a shekara mai zuwa?

2022-09-20 21:29:44 CMG Hausa

Kwanan nan wani jami’in ofishin kamfanin samar da kofi na kasar Vietnam dake birnin Shanghai na kasar Sin, ya ce yanzu suna da dillalai sama da 300 a kasar wadanda ke taimakawa sayar da kofi.

An kawo karshen bikin baje-kolin Sin da kungiyar ASEAN ko kuma CAEXPO, kana taron kolin Sin da ASEAN a fannin kasuwanci da zuba jari karo na 19, a jihar Guangxi ta kasar Sin a jiya Litinin. A cikin kwanaki hudu, kamfanoni 1653 na kasashe 40 sun halarci taron, har ma akwai kamfanoni sama da dubu 2 da suka hallara ta kafar intanet, inda aka kulla ayyukan hadin-gwiwa 267, kana, jimillar kudin da aka zuba a wadannan ayyukan ta kai kudin Sin Yuan biliyan 413, wanda ya kai matsayin koli a tarihi. Ke nan an cimma nasarori masu tarin yawa a wajen bikin CAEXPO a bana.

A halin yanzu, tattalin arzikin duniya na fama da koma-baya, har ma asusun bada lamuni na duniya IMF, da sauran wasu cibiyoyin duniya, duk sun rage hasashen da suka yi, kan karuwar tattalin arzikin duniya a bana da shekarar badi. A irin wannan yanayin da ake ciki, shirya bikin CAEXPO na da ma’ana ta musamman.

A yayin da wasu kasashe masu karfin tattalin arziki ke kokarin rufe kofarsu, kasar Sin ta gudanar da bikin CAEXPO, al’amarin da ya samar da sabbin damammaki ga farfadowar tattalin arziki, bayan da aka kawo karshen annobar COVID-19. (Murtala Zhang)