logo

HAUSA

Mataimakin shugaban kasar Sin ya halarci jana’izar sarauniyar Ingila Elizabeth II

2022-09-20 20:53:07 CMG Hausa

Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin shugaban kasar ta Sin Wang Qishan, ya halarci jana’izar sarauniyar Ingila Elizabeth II, wadda aka gudanar a jiya Litinin a birnin Landan.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar a Talatar nan, ta ce Wang ya halarci jana’izar da aka yi a cocin Westminster, tare da sauran manyan shugabannin kasashen duniya, da iyalan gidan sarautar, da wakilan gwamnatoci da dama. Kaza lika sanarwar ta ce, da yammacin ranar Lahadi, Wang ya shiga zauren majalissar dokokin Birtaniya, inda aka ajiye gawar sarauniyar, domin baiwa manyan baki damar yin ban kwana da ita gabanin binne ta. (Saminu Alhassan)