Grace Boukete: Afirka na bukatar abin koyi, kuma Sin ta cancanci zama
2022-09-19 21:31:41 CRI
Grace Boukete saurayi ne da ya fito daga jamhuriyar Congo, wanda kawo yanzu ya shafe tsawon shekaru 3 yana dalibta a kasar Sin, har ma ya samu suna na Sinanci, wato Gao Xiang.
Ya ce, “Kasar Sin ta samu gagaruman nasarori wajen bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma, wanda kuma ke haifar da babban tasiri ga duniya. Duk wata kasar da take fatan ganin samun ci gaba da albarka, to, ya kamata ta kalli kasar Sin. Kasashenmu na Afirka na bukatar abin koyi, don haka, na mai da hankalina a kan kasar Sin.”(Lubabatu)