logo

HAUSA

Li Yi: Jin dadin gudanar da aikin gona a Afirka

2022-09-19 14:23:09 CMG Hausa

Li Yi mai shekaru 27, ‘yar asalin garin Nantong ce, wanda ke lardin Jiangsu na gabashin kasar Sin. A baya, tana aiki ne da kamfanin McKinsey. Saboda sha’awarta ga nahiyar Afrika, Li ta nemi a sauya mata wajen aiki daga ofishin birnin Beijing, zuwa na Nairobin Kenya, a 2019. A farko 2021 kuma, ta bar aiki, ta shiga kasuwanci a fannin aikin gona a Nairobi. Li ta ce, “a ganina harkar gona ta nahiyar Afrika na da dimbin damarmaki, don haka nake son gwadawa.”

Li ta yi ammana cewa, mutane da dama na da sabbin dabaru, amma ba su da damar nunawa. A ganinta, ta yi sa’ar samun damarmaki. Tun da ta bar garinsu tana da shekaru 15, domin shiga makarantar sakandare a Nanjing, babban birnin lardin Jiangsu, Li ke zuwa sabbin wurare, da ganin sabbin yankunan da sabbin rayuwa. Kamar galibin iyaye Sinawa, iyayenta na mayar da hankali kan kwazonta a makaranta a ko da yaushe. Amma mahaifiyarta na yawaita tambayarta, “Yau kin ji dadin makaranta?” maimakon “ko kin samu sakamako mai kyau a jarrabawa?”A don haka, tana jin dadi saboda mahaifiyarta na taimaka mata wajen zama mai kwarin gwiwa da farin ciki a rayuwa.

Yayin hutun lokacin rani na farko a sakandare, Li Yi ta halarci wani taron horo a Amurka. Bayan dawowarta kuma, ta kafa wata kungiyar kula da muhalli a makarantarsu. Har yanzu tana iya tunawa da lokacin da kungiyar ta zo ta biyu yayin wata gasar kare muhalli, an kuma gayyaci mambobin kungiyar su shiga aikin shuka bishiya a jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta, dake arewacin kasar Sin.

Tun daga lokacin da take makarantar sakandare, Li ta koyi tsara shirye-shirye da tuntubar mutane da hada mutane su gudanar da wani aiki tare.

A shekarar 2012, Li ta samu gurbin karatu a kwalejin Pomona ta California dake Amurka. A lokutan hutu da shirye-shiryen musayar dalibai, ta ziyarci gomman kasashen Amurka da Turai. ta bayyana cewa, ”kowacce tafiya cike take da labarai, kuma na kara gogewa wajen tafiya ni kadai. Da na daina tsoron wuraren da ban taba zuwa ba, sai kofar duniya ta bude a gare ni, ta wata hanya ta daban.”


A wani zango gabanin kammala karatu, Li ta samu wani aikin wucin gadi a wata gona. Wannan shi ne karo na farko da ta shiga aikin gona, kuma karon farko da ta fahimci wahalar aikin. “idan da wani ya fada min a baya cewa, shekaru 5 bayan sannan zan ci gaba da aikin gona a Afrika, da ba zan yarda ba” cewarta.


Bayan Li ta kammala karatu a jami’ar Pomona a watan Yunin 2016, sai ta fara aiki a ofishin kamfanin McKinsey dake Los Angeles, wanda ke bada shawarwari ga galibin fitattun cibiyoyin kasuwanci na duniya. Bayan shekara guda a Los Angeles, Li ta sauya kasa saboda ba ta samu bizar aiki ba. Za ta iya fita daga kasar, sai bayan shekara guda ta koma. Don haka, a shekarar 2017, aka mayar da Li ofishin birnin Beijing. Yayin da sauyin wajen aiki ya dauki lokaci, Li ta yanke shawarar daukar hutu. Ta yi tafiye-tafiye a kasar Sin, kuma ta ziyarci kasashe da dama a kudu maso gabashin Asiya. Li ta fara aiki a ofishin Beijing ne a watan Janairun 2017.

Shekara guda bayan nan, kamfanin ya sanar da ita za ta iya komawa Amurka, saboda an amince da bizarta. Amma Li ba ta koma ba, saboda a ganinta, aiki a kasashe masu tasowa zai fi ban sha’awa. Don haka, aka tura ta aiki a ofishin kamfanin dake Nairobi, a karshen wata Agustan 2019. Li ta ce, “a ganina, aiki a Kenya ya fi ban sha’awa da kalubale, domin na shiga wasu ayyuka da dama a matakin kasa a kasar.”

A karshen 2020, Li ta yi tunanin fara nata kasuwancin. Shugabanta ya sanar da ita cewa, daya daga cikin kamfanonin aikin gona da ya zubawa jari na neman abokin hulda. Sai Li ta ga cewa kamfanin ya dace da bukatunta. A watan Afrilun 2021, ta hada hannu da kamfanin da ya fara harkokin aikin gona, a matsayin daya daga cikin wadanda suka asassa kamfanin, inda take kula da bangaren tafiyar da ayyuka da kuma talla. Li ta ce, “A ganina, bangaren noma na Afrika na da dimbin damarmaki. Fara kasuwanci ya bambanta da aikin bayar da shawara. Duk da cewa manufarsu dukka ita ce warware matsalolin kasuwanci, fara kasuwanci na bukatar ‘yan kasuwa su san hakkin da ya rataya a wuyansu na mallakar sana’ar. A wannan kamfani, ina jin cewa, ina girma tare da shi.”

Iyaye da kawayen Li ma na son ta samu wani sabon muhallin da za ta samu ci gaba cikin sauri, kuma ta kara kalubalantar kanta. Da farko, gona eka 30 kadai suke da ita. Li ke kula da kusan komai, ban da girbi. Har yanzu tana iya tunawa da karo na farko da ta ziyarci gonar, ta kadu da ganin yadda ma’aikata ke kididdige bayanai a kan takarda.  Saboda ta inganta aikin nasu, sai ta koya musu yadda za su adana bayanai a kan na’urar kumfuta. 


Manufar kamfaninsu ita ce, samar da kayayyakin lambu masu kyau da inganci ga kasuwar cikin gida. Abubuwan da suke samarwa sun hada da tattasai da yalo da dankali da tumatir da gurji da sauransu. Yanzu, jimilar girman gonakinsu 3, ya kai eka 165, da katafaren dakin adana kayayyaki da ma’aikata sama da 400. Daya daga cikin gonakinsu na da nisan tafiyar awa 2 daga Nairobi. Suna da direbobi 6 da manyan motocin daukar kaya 5, kuma direbobin na jigilar kayayyakin lambu kimanin ton 10 a kowacce rana. 


Kamfaninsu ya shiga ayyukan gona sama da 600 a Kenya. Su kan yawaita tsarawa manoman yankin kai ziyarar gonaki da dakin adana kayayyaki na kamfaninsu, da halarta kwasa-kwasan horo domin koyon yadda ake noman kayayyakin lambu a kimiyyance. Suna kuma sayen kayayyakin lambu daga wajensu.


Kamfanin Li kan girbe tare da rarraba kayayyakin lambu a rana guda, sannan su kai kasuwa washegari da asuba. Don haka, kasa da sa’o’i 24 ake bukata wajen jigila, daga gona zuwa kasuwa. Sun kuma kafa wani tsari na bibiyar kayayyaki. Misali, idan aka samu rubabben tumatir, za su iya gano daga gonar da ya fito da kuma wanda ya yi aikin rarrabawa.

Abokin kasuwancin Li dan kasar kenya, Peter Mouchy, gogaggen dan kasuwa ne da ba ya kasa a gwiwa wajen kara ilimi da amincewa sabbin dabaru. Shi ne yake kula da aikin bayar da horo da girbi. Ya ce zuwan Li kamfanin, ya taimakawa ci gabansa. Kamfaninsu ya amfana da gogewa da fasahohin kasar Sin da dama, kamar shuka cikin kebabben wuri, da amfani da injin ban ruwa mai sarrafa kansa da na’urorin feshi masu sarrafa kansu.

Li na ganin hadin gwiwarsu a kamfanin, na moriya juna ne. Ta ce, ”saboda na zauna a kasashe da dama, na iya mu’amala da mutane masu al’adu daban-daban. Babu wata matsala ta fahimta a tsakaninmu, kuma na koyi abubuwa da yawa daga abokaina na kasar Kenya. Da yawa daga cikinsu na da kyakkyawan fata kuma ba sa fargaba.”

Li na fatan kamfaninsu zai iya lalubo dimbin damarmakin da aikin gona ke tattare da su a Afrika, da kuma taimakawa mutanen kasar inganta rayuwarsu ta hanyar raya aikin gona. Li ta kara da cewa, “tun da na fara aiki a bangaren aikin gona a shekarar 2021, ban dauki hutu sosai ba, kuma kasashen da na ziyarta ba su da yawa, amma ina kan wani tafarki ne na cimma burina, haka kuma na samu damar morar abubuwa daban daban, na ji dadi.”(Kande Gao)