logo

HAUSA

Sabon Firaminsitan Senegal ya kafa gwamnati

2022-09-19 11:03:40 CMG Hausa

Sabon Firaministan kasar Senegal Amadou Ba, ya kafa gwamnati mai kunshe da mambobi 38, da yammacin ranar Asabar.

Ministan kula da harkokin gwamnatin kasar, Abdou Latif Coulibaly ne ya sanar da haka ga manema labarai da yammacin ranar.

An nada Amadou Ba matsayin firaminista ne da safiyar ranar Asabar, inda ya bayyana yayin nadin cewa, aikin gwamnatinsa shi ne neman cimma burin shugaban kasar Macky Sall, wanda ke mayar da hankali kan aiwatar da shirin nan na Senegalese Emerging Plan na shekaru 10 da aka kaddamar a shekarar 2014 da nufin gaggauta ci gaban kasar.

Gwamnatin baya dai ta kunshi ministoci 33 da mataimakan ministoci 4.

Bisa wata dokar shugaban kasa da aka fitar da safiyar Asabar din ne aka nada Amadou Ba matsayin Firaminista, mukamin da aka soke a shekarar 2019, aka kuma dawo da shi a bara.

Sabon firaministan mai shekaru 61, ya taba rike mukaman ministan tattalin arziki da harkokin kudi da kuma na harkokin wajen kasar. (Fa’zia Mustapha)