logo

HAUSA

Kalaman John Kerry sun nuna girman kai na kasashen yamma

2022-09-19 21:05:20 CMG Hausa

Kalaman da manzon musamman na shugaban kasar Amurka mai kula da aikin tinkarar sauyawar yanayi John Kerry ya furta, a taron ministocin kasashen Afirka kan aikin kare muhalli, wanda ya gudana a kasar Senegal a kwanan baya, sun ba ni mamaki sosai. Saboda a gaban wakilan dukkan kasashen Afirka, mista Kerry ya ce kasashe masu sukuni, ba su da wani nauyi na tarihi game da batun sauyawar yanayin duniya.

A ganinsa, aikace-aikace na daukacin dan Adam ne ke sa ake samun matsalar dumamar yanayi, saboda haka, ko da wata kasa dake fama da koma bayan tattalin arziki a nahiyar Afirka, wadda ke jin radadin bala’i daga Indallahi da sauyawar yanayin duniya ta haddasa, ya kamata ta dauki nauyi na tinkarar matsalar sauyawar yanayin da kan ta. Kana kasashe masu sukuni ba sa bukatar biyan diyya ga kasashen masu tasowa.

To amma mene ne gaskiyar wannan batu? Sanin kowa ne, sannu a hankali, aikace-aikacen dan Adam na yin tasiri kan muhallin duiya. Tun kafin kasashe masu tasowa su fara raya masana’antunsu, kasashen yamma masu sukuni sun riga sun kwashe shekaru fiye da 200, suna kokarin bunkasa bangaren masana’antu, tare da fitar da dimbin iska mai dumama yanayi, da gurbata muhallin duniya sosai. Hakan ya sa dukkan kasashe masu tasowa ke dauke da ra’ayin cewa, kamata ya yi, kasashe masu sukuni, da kasashe masu tasowa su dauki nauyi na bai daya, amma masu bambanci da juna, a yayin da ake tinkarar batun sauyawar yanayi. Wannan ra’ayi ya nuna adalci, da dacewa da al’adar mutanen duniya, ta sanya wanda ya gurbata muhalli biyan diyya.

Sai dai maganar Kerry ta saba wa wannan ra’ayi na bai daya na daukacin kasashe masu tasowa. Lamarin da ya sanya ‘yan Afirka fushi sosai: Wasu kungiyoyin jama’a da yawa na kasashe fiye da 40 dake nahiyar Afirka, sun nuna takaicinsu, inda suka ce John Kerry ya yi wasan fatar baki ne kawai, kana ya halarci taron ne don neman janyo hankalin mutanen duniya kan huldar dake tsakanin Amurka da kasashen Afirka.

Hakika, zancen Kerry ya nuna yadda kasar Amurka, da sauran kasashen yamma suke da girman kai. A ganinsu, yadda kasashe masu tasowa suke tsayawa kan samun adalci, wani yunkuri ne na neman kudi kawai.

Ban da wannan kuma, Kerry ya yi gargadi ga kasashen Afirka, cewa kar su zuba kudi da yawa a aikin hakar iskar gas, duk da cewa akwai kasashen Afirka da yawa da suke kokarin raya bangaren iskar gas, don tabbatar da tsaron makamashi. A cewar John Kerry, ya kamata a raya makamashi da ake sabuntawa, maimakon iskar gas. Ya ce, “kar ku maimaita kurakuran da muka yi a baya.” Nufinsa shi ne, saboda kasashen yamma sun taba yin kurakurai, don haka a yanzu sun fi sanin hanya mai dacewa da ya kamata a bi ta. Ya kamata kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa su bi umarnin kasashen yamma. A nan an nuna girman kai matuka.

Ta hanyar sauraron maganar John Kerry, za mu gane cewa, aikin tinkarar sauyawar yanayi ba shi da sauki. Kuma ba za a cimma nasara ba, sai dai in kasashen yamma daina nuna girman kai da son kai, sa’an nan su yi cudanya da kasashe masu tasowa cikin daidaito. (Bello Wang)