logo

HAUSA

Yaushe kasashen yamma za su iya daukar nauyin da ke bisa wuyansu

2022-09-18 21:36:34 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Kwanan baya, an gudanar da taron kolin kasashen Afirka game da daidaita matsalar sauyin yanayi a birnin Rotterdam na kasar Netherlands, inda shugabannin kasashen Afirka guda shida suka hallara, a yayin da firaministan kasar Netherland shi kadai ya halarci taron, ba tare da shugabannin sauran kasashen yamma da aka ba su goron gayyata ba, ciki har da Faransa da Norway da Canada da sauransu.

Hakan ya bakanta ran shugabannin kasashen Afirka. Shugaban kasar Senegal Macky Sall, wanda kuma shi ne shugaban karba karba na kungiyar tarayyar Afirka, ya furta a wajen bikin bude taron cewa, “Abin bakin ciki shi ne, na lura da rashin hallarar shugabannin kasashe masu ci gaban masana’antu a wajen taron. Na yi zaton idan mun yi kokari mun bar Afirka har mun zo Rotterdam, to, mutanen kasashen Turai da sauransu za su fi samun saukin halartar taron.” Shugaban jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, shi ma ya yi suka cewa, “Sanin kowa ne su ne suka fi lalata yanayin duniyarmu.”

Abun hakan yake, kafin kasashe masu tasowa suka fara raya masana’antu, tuni masana’antun kasashe masu sukuni na yammacin duniya suka fara fitar da iska mai gurbata muhalli a shekaru kusan 200 da suka wuce. Dan tasiri kadan ne kasashen Afirka, da ma sauran kasashe masu tasowa suka haifar ga sauyin yanayin duniya, amma illolin da sauyin yanayin ke haddasawa sun fi addabarsu. A sabo da haka, kasashen duniya sun cimma yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD da ma yarjejeniyar Paris, wadanda suka bukaci kasashe masu ci gaba su dauki matakai na kayyade iskar Carbon da suke fitarwa, tare kuma da samar da kudade da ma fasahohi ga kasashe masu tasowa wajen daidaita matsalar. Sai dai abin takaici shi ne, ba a aiwatar da yarjejeniyoyin yadda ya kamata ba, kuma kasashen Turai da Amurka ma sun gaza cika alkawuransu, na taimakawa kasashe masu tasowa wajen tinkarar sauyin yanayi.

Rashin hallarar shugabannin kasashen yamma a wajen taron, ya shaida yadda suke rashin girmama kasashen Afirka a kullum, baya ga kuma yadda suke gudun daukar nauyin da ke bisa wuyansu. Ba kawai sauyin yanayi na shafar makomar kasashen Afirka ba ne, har ma yana shafar makomar bai daya ta ‘yan Adam da ta duniyarmu baki daya. Kamar dai yadda Amina Mohammed, mataimakiyar babban sakataren MDD ta bayyana a wajen taron, “da fika-fikai biyu ne tsuntsu ke iya tashi”, dole ne kasashen Yamma su gane cewa, makomar dan Adam daya ce, kuma su cika alkawuran da suka dauka, tare da daukar nauyin da ke bisa wuyansu, ta fannin daidaita matsalar sauyin yanayi.”(Mai Zane:Mustapha Bulama)