Kungiyar SCO na tabbatar da zaman lafiya a duniya
2022-09-18 16:52:17 CMG Hausa
A ranar 16 ga watan da muke ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin jawabi, a wajen taro na 22, na majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO, inda ya nanata bukatar ci gaba da tsayawa kan ruhin Shanghai, don kyautata ayyukan kungiyar.
Hakika, bayan da aka kwashe shekaru 21 ana kokarin raya harkokin kungiyar SCO, ta riga ta zama wata babbar kungiyar hadin gwiwa, wadda ta shafi mafi girman yanki, da mafi yawan mutane a duinya.
Dalilin habakar kungiyar SCO shi ne nacewar ta kan wasu manyan manufofi, wadanda suka hada da amincewa da juna a fannin harkokin siyasa, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna, da zaman daidai wa daida, da bude kofa ga kasashen ketare, da hakuri da mabambantan ra’ayoyi, gami da kokarin tabbatar da adalci a duniya.
Wadannan manufofi sun sa kungiyar SCO zama wani dandalin da ake musayar ra’ayoyi tsakanin wayewar kai ta kasashe daban daban, da girmama juna, da mutunta turbar da duk wata kasa ta zaba don raya kanta, da kula da moriyar dukkan bangarori, da gudanar da tattaunawa a tsakaninsu don magance sabanin ra’ayi.
Ko da yake duniyarmu na cikin wani yanayi mai wuya, amma ruhin Shanghai zai kara taka muhimmiyar rawa, wajen taimakawa al’ummun duniya wajen daidaita matsalolin da suke fuskanta. (Bello Wang)