logo

HAUSA

Mali ya ki amincewa a shiga tsakani kan batun tsare sojojin Kwadibuwa

2022-09-17 16:02:21 CMG Hausa

A ranar 15 ga wata, gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali ta yi fatali da kiran da kasar Kwadibuwa ta yi, na shirya taron gaggawa game da rikicin yankin, kan tsare sojojinta, ta kuma yi kashedi cewa, kungiyar ECOWAS ba ta daidaita batun dake tsakanin bangarori biyu bisa adalci ba. Tana mai cewa, gwamnatin Togo za ta taimaka wajen daidaita matsalar wadda ta riga ta kasance shishigin diflomasiyya.

Shugaban kasar Kwadibuwa Alassane Ouattara ya kira taron kwamitin tsaron kasar a ranar 14 ga wata, daga baya kwamitin ya fitar da wata sanarwa, inda aka yi kira da a kira taron kolin shugabannin kasashen yammacin Afirka cikin gaggawa, domin tattauna batun tsare sojojin Kwadibuwa da yawansu ya kai 46 da Mali ta yi. Amma Mali ya ki yarda da lamarin.

A ranar 10 ga watan Yulin bana ne, aka kama sojojin Kwadibuwa 49 da suka isa filin jirgin saman Bamakon kasar Mali, saboda gwamnatin wucin gadin Mali ta ayyanasu a matsayin sojojin haya, kuma za ta kai su gaban kotu, gwamnatin Kwadibuwa ta bukaci Mali da ta saki sojojin nan take, daga baya Mali ta saki sojoji mata guda uku dake cikinsu. (Jamila)