logo

HAUSA

Farfadowar tattalin arzikin kasar Sin ya zarce yadda ake tsammani

2022-09-16 20:44:37 CMG Hausa

Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar Jumma’ar nan sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar ya ci gaba da farfadowa a cikin watan Agusta, kuma dukkan manyan ma’aunai dake alanta bunkasar tattalin arzikin sun inganta. Daga cikin su, yawan motocin da ake samarwa ya karu da kashi 39 cikin 100, haka kuma karin darajar masana'antar kera motoci, shi ma ya karu da fiye da kashi 30 cikin 100.

Kafofin watsa labaru na ketare sun bayar da rahotanni fiye da yadda ake tsammani, wajen bayyana yadda tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba a cikin watan Agusta.

Ma’aunan su ne ake dubawa, wajen hada jimillar kayan masarufi da aka sayar, da karin kimar masana'antu na kasa sama da girman da aka ware, da hannayen jarin da aka saka, da sauransu. Ma’aunai biyu na farko sun karu kan na shekarar 2021 a cikin Agusta bi da bi. Wato kaso 5.4 cikin 100, da kuma kaso 4.2 bisa 100, yayin da jarin da aka saka a bangaren kadari, ya karu da kaso 5.8 cikin 100 a cikin watanni 8 na farkon shekara. (Ibrahim)