logo

HAUSA

Hajojin Zimbabwe dake shiga Sin sun karu da kaso 7.5

2022-09-16 10:39:11 CMG Hausa

Hukumar kididdiga ta Zimbabwe ko Zimstat, ta ce adadin hajojin da Zimbabwe ke shigarwa kasar Sin sun karu daga kaso 6.7 bisa dari a watan Yuni, zuwa kaso 7.5 bisa dari a watan Yuli.

Zimstat ta ce alkaluma sun nuna yadda Sin ta zama kasa ta 3 mafi girma, a fannin hada hadar cinikayya da Zimbabwe, baya ga Afirka ta kudu, da Hadaddiyar daular Larabawa. Kaza lika Sin din ce ke sayen ganyen taba mafi yawa daga Zimbabwe.

A baya bayan nan, ofishin jakadancin Sin dake Zimbabwe, ya ce cikin watanni 7 na farkon shekarar bana, Sin ta shigo da albarkatun gona daga Zimbabwe, wadanda darajarsu ta kai na dalar Amurka miliyan 332, adadin da ya karu da kaso 111.6 cikin shekara guda.  (Saminu Alhassan)