logo

HAUSA

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya kai sama da kaso 20 a watan Augusta

2022-09-16 11:32:38 CMG Hausa

Hukumar kididdiga ta Nijeriya ta ce yawan hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya kai kaso 20.25 cikin dari a watan Augusta, adadi mafi yawa tun bayan watan Satumban 2005.

Rahoton da hukumar ta fitar a jiya, ya ce alkaluman farashin kayayyakin masarufi a kasar, wandanda su ne manyan ma’aunan hauhawar farashin kayayyaki, sun karu da kusan maki kaso 3.5 daga kaso 17.01 da aka samu a watan Augustan 2021.

A cewar rahoton, abubuwan da suka haddasa karuwar hauhawar farashin sun hada da tsaiko tsarin samar da kayayyakin abinci, yayin da sauran wasu abubuwa suka haddasa karuwar farashin shigar da kayayyaki kasar saboda ci gaba da faduwar darajar takardar kudin kasar da kuma karuwar daukacin farashin sarrafa kayayyaki. (Fa’iza Mustapha)