logo

HAUSA

Joao Lourenco na Angola ya sha rantsuwar kama aiki a karo na biyu

2022-09-16 11:14:56 CMG Hausa

Zababben shugaban kasar Angola Joao Lourenco ya sha rantsuwar kama aiki a karo na biyu a matsayin shugaban kasar, jiya Alhamis, yayin wani biki da ya gudana a Luanda, babban birnin kasar.

Joao Lourenco na jam’iyyar MPLA mai mulkin kasar Angola, ya sha rantsuwar ce a gaban a kalla shugabannin kasashe da wakilai 12.

An kuma baza jami’an tsaro a muhimman tituna da wurare yayin bikin rantsuwar. (Fa’iza Mustapha)