logo

HAUSA

Kowa Ya Yi Da Kyau Zai Ga Da Kyau

2022-09-15 15:00:31 CMG HAUSA

Daga Ibrahim Yaya

Yayin da tattalin arzikin wasu kasashen duniya ke kara fuskantar matsin lamba da tangal-tangal sakamakon manufofin marasa dacewa da tasirin annobar covid-19 da makamantansu, a hannu guda kuma wani rahoto da hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar ya nuna cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin yanayi na daidaito da bunkasuwa yadda ya kamata, kana baki dayan karfin kasar ma ya ingantu matuka, haka kuma tasirinsa a duniya yana karuwa a kai a kai. Wannan ya kara tabbatar da ingancin matakan da mahukuntan kasar ke dauka game da raya tattalin arziki da ma sauran fannoni na ci gaban kasa.

Alkaluma na nuna cewa, daga shekarar 2013 zuwa 2021, GDPn kasar Sin ya karu da kashi 6.6 bisa dari a duk shekara, wanda ya zarce matsakaicin karuwar kashi 2.6 cikin 100 a duniya, da kashi 3.7 cikin 100 na kasashe masu tasowa a makamancin wannan lokaci, sabanin yadda wasu kasashen yamma ke fama da matsaloli na hauhawar farashin kaya da rashin aikin yi.

Kasar Sin dai ta nace kan inganta ci gaba mai inganci, da bude kofa ga ketare, da sassauta hanyoyin shiga kasuwanninta a bangaren samar da hidima, da bude harkokin cinikayya tsakanin kasashe, da fadada aikin dandalin bude kofa ga waje, baya ga kokarin da take yi na kafa ingantaccen tsarin fadada sashin samar da hidima.

A baya-bayan nan ma firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar aiwatar da manufofin daidaita tattalin arziki, da farashin kayayyaki, da samar da guraben ayyukan yi. Matakan da masana ke cewa, kyakkyawar dabara ce da za ta haifar da da mai ido.

Duk da cewa daidaituwar tattalin arziki ya danganta da yanayin hada-hadar kasuwanni, akwai bukatar a kara azama, wajen rage wahalhalun da sashen hada hadar kasuwannin ke fuskanta, yayin da ake kara fadada harkokin zuba jari, har a kai ga samar da damammakin bunkasa kasuwanni, da karfafa kwarin gwiwarsu.

Idan har ana fatan cimma burin raya tattalin arziki da zai faranta ran al’umma da ma farfado da tattalin arzikin duniya baki daya, ya dace a kara azama wajen kammala manyan ayyuka, da fadada hada-hadar kudade bisa tsare-tsare da aka tanada gwargwadon bukatun cikin gida. Kana martaba dokokin hadin gwiwar kasa da kasa da muradun juna da sahihin hadin gwiwa, na daga cikin abubuwa da za su taimaka wajen samun farfadowar tattalin arzikin duniya, wanda daga karshe zai taba rayuwar bil-Adama baki daya daga dukkan fannoni. Don haka, duk wanda ya yi da kyau shi ma zai ga da kyau. (Ibrahim Yaya)