logo

HAUSA

Masana sun yabawa huldar Sin da Afrika a fannin fasahohin makamashin rana

2022-09-15 10:56:50 CMG Hausa

Masana da masu tsara manufofi, sun yabawa huldar dake akwai tsakanin Sin da Afrika a fannin amfani da fasahohin makamashin hasken rana.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, darakta janar na kungiyar kawancen kasashe domin amfani da makamashin rana ta duniya (ISA), Ajay Mathur, ya jaddada muhimmancin hulda da Sin da dimbin damarmakin da hakan ke da shi wajen cimma burin nahiyar Afrika na raya makamashin hasken rana.

Da yake bayyana karancin samar da kananan turakun makamashin hasken rana a duniya, Ajay Mathur ya yi kira ga kamfanonin kasa da kasa, su mayar da hankali wajen samar da tashoshin makamashin hasken rana da ba su dogara da turakun lantarki ba a nahiyar, domin jama’ar dake yankunan karkara da wurare masu nisa su amfana.

Ya ce kasar Sin ce ke kan gaba wajen samar da kayayyakin samar da makamashin hasken rana a fadin duniya, musamman a Afrika. Yana mai cewa faifan samar da lantarki daga hasken rana wato Panels da baturan da ake amfani da su a Afrika, sun fito ne daga kasar Sin.

A cewarsa, nahiyar na da dimbin damarmakin makamashin da ake iya sabuntawa, ciki har da arzikin hasken rana.

Kungiyar ISA ta gudanar da taron kwamitin shiyya karo na 4 ne a Addis Ababa na Habasha a karshen watan Augusta, inda ya samu halartar ministocin makamashi na kasashen nahiyar, domin tattauna hanyoyin samar da mafita mai dorewa ga karancin makamashi a nahiyar, ta hanyar amfani da albarkatun hasken rana. (Mai Fassarawa: Fa’iza Mustapha)