An dakile yunkurin Amurka da Burtaniya da Australia ta fannin nukiliya
2022-09-14 11:21:10 CMG Hausa
A karo na 4 a jere, an cimma daidaito kan ayyana abun da ke shafar hadin gwiwa tsakanin kasashen Amurka, da Birtaniya da Australiya, a matsayin batun da za a tattauna a hukunce,a gun taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA), wanda ya gudana a ranar 12 ga wata. Matakin da ya shaida cewa, hadin gwiwar kasashen uku ta fannin jiragen karkashin ruwa masu amfani da makamashin nukiliya, ba abu ne na kansu ba. A maimakon haka, ya kamata hadin gwiwar ya gudana a karkashin kulawar kasashe mambobin hukumar.
Hadin gwiwar da ya shafi jiragen karkashin ruwa masu tafiya da makamashin nukiliya, na shafar tataccen sinadarin Uranium, wanda ake iya amfani da shi wurin kera makamai, da ma fasahohi da na’urorin da abin ya shafa, matakin da ka iya haifar da yaduwar nukiliya, wanda kuma ya saba yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya. Don haka, ya zama dole dukkanin kasashe mambobin hukumar su tattauna, tare da tsai da kuduri a kai.
Yadda aka dakile yunkurin kasashen Amurka da Burtaniya da Australia karo hudu a jere, ya shaida cewa, kowa ya gane yadda Amurka da Burtaniya ke nuna fuska biyu a kan batun nukiliya, inda a sa’i daya, suka bayyana damuwarsu a kan batun nukiliyar Koriya ta arewa da na Iran. A sa’i dayan kuma, suka yi na’am da hadin gwiwa da Australia, wajen jiragen karkashin ruwa masu tafiya da makamashin nukiliya.
Mene ne kawancen Amurka da Birtaniya da Australia ke nema a yankin Asiya da tekun Pasifik? Lallai kowa ya san suna neman tada rikici ne a yankin, kamar dai yadda kungiyar NATO ta yi. (Lubabatu Lei)