logo

HAUSA

Najeriya ta sha alwashin kara yawan sha zawa da take nomawa

2022-09-14 11:20:46 CMG Hausa

 

Ministan ma’aikatar cinikayya masana’antu da zuba jari na tarayyar Najeriya Adeniyi Adebayo, ya ce gwamnati ta tsara aiwatar da matakan da za su bunkasa noman sha zawa ko Cashew a kasar, ta yadda adadin gyadar sha zawan da kasar ke samarwa zai karu da tan 240,000, zuwa jimillar tan 500,000 a duk shekara.

Cikin wata sanarwa da ministan ya fitar, ya ce gwamnatin Najeriya na fatan za a rika sarrafa a kalla kaso 50 bisa dari na gyadan sha zawar, wadda a yanzu yawan wadda kasar ke samarwa ba ta wuce tan 260,000 ba.

Minista Adebayo ya jaddada cewa, hanya daya tilo ta fadada gudummawar da noman gyadar sha zawar ke bayarwa ga tattalin arzikin Najeriya ita ce ta sarrafa danyar gyadar sha zawa, domin ta haka ne za a iya wanzar da ci gaban noman dan itacen, matakin da zai bude sabuwar kasuwar sabbin hajoji masu nasaba da Cashew, tare da samar da karin guraben ayyukan yi, da samar da arziki ga ’yan kasa. (Saminu Alhassan)