logo

HAUSA

An Kaddamar da Mataki na 2 Na Aikin Kafa Fitilu Masu Amfani Da Hasken Rana Na Ba Da Hannu Ga Motoci A Abuja

2022-09-14 11:38:57 CMG Hausa

An yi bikin kaddamar da mataki na 2 na aikin kafa fitilu masu amfani da hasken rana na ba da hannu ga motoci a birnin Abuja, hedkwatar kasar Najeriya jiya Talata 13 ga wata, wanda kasar Sin ta ba da gudummowar gudanarwa.

Jakadan kasar Sin a Najeriya Cui Jianchun, da babban sakatare a hukumar kula da babban birnin tarayyar Najeriya Abuja Adesola Olusade, da ma wasu jami’an Sin da Najeriya sun halarci bikin.

A yayin bikin, jakada Cui ya ce, aikin yana cikin matakai masu nasaba da manyan ayyuka 9 da aka sanar, a taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kana wani muhimmin bangare ne  cikin manyan tsare-tsaren hadin gwiwa a tsakanin Sin da Najeriya. Sa’an nan kuma, aikin alama ce ta dankon zumunci a tsakanin kasashen 2.

A nasa bangare, Adesola Olusade, ya jinjinawa kasar Sin, bisa taimakon da ta dade tana bayarwa. Ya ce aikin zai sassauta matsin lambar da ake fuskanta a Abuja, da kyautata zirga-zirgar birnin, da rage yawan hadarurrukan mota, da kuma saukaka zaman rayuwar mazauna birnin sosai. (Tasallah Yuan)