logo

HAUSA

Matakan Kasar Sin na kare hakkin bil-Adama

2022-09-14 09:31:32 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya nada Volker Turk, dan kasar Austria a matsayin babban kwamishin hukumar kare hakkin bil-Adama ta MDD, bayan samun amincewar babban taron majalisar, domin maye gurbin Michelle Bachelet, ’yar kasar Chile, bayan karewar wa’adin aikinta.

Bayan sanar da nadin Turk kan wannan mukami, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya bayyana fatan cewa, Turk zai jagoranci hukumar wajen gudanar da ayyukanta kamar yadda doka ta tanada.

Kalaman Dai Bing na zuwa ne, bayan da aka zargi hukumar da kokarin siyasantar da batun da ya shafi kare hakkin bil-Adama. Kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa, sun nuna damuwa matuka game da rashin daidaiton ma’aikata a ofishin hukumar, da yadda kasashe masu tasowa ba su da wakilcin da ya dace a hukumar.

Don haka, bangaren kasar Sin ke kira da a yiwa hukumar kwaskwarimar da ta dace, dom ganin an dama da kowa da kowa a harkokin hukumar.

Idan ba a manta ba, a wannan shekara ce, jami’ar hukumar mai shirin barin gado Michelle Bachelet ta ziyarci yankin Xinjiang na kasar Sin, kuma a cikin rahoton da ta fitar a ranar 28 ga watan Mayun bana, bayan da ta kammala ziyararta a jihar Xinjiang ta kasar Sin ta yaba wa kasar Sin, kan kokarinta a fannonin rage talauci, da kare mutane marasa karfi, da yunkurin tabbatar da ingancin hakkin dan Adam, da sauransu.

Amma daga bisani, sai ofishin hukumar ya fitar da sabanin wannan rahoto, matakin dake zama tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da amfani da batun kare hakkin bil-Adam don neman shafawa kasar Sin bakin fenti da neman mayar da hannun agogo baya, a kokarin da kasar Sin ke yi na kare hakkin daukacin bil-Adama bisa doka.

Kasar Sin dai ba ta boyewa duniya shirye-shiryenta na inganta rayuwar al’ummar Xinjiang dake shafar yaki da ayyukan ta’addanci ba, matakan da a lokuta da dama suka samu yabo daga kasashen duniya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)