Binciken kariyar cutar COVID-19 a jiki ya nuna cewa, yawancin yara Amurkawa sun taba kamuwa da cutar
2022-09-14 07:49:54 CMG Hausa
Shafin mujallar Nature ta kasar Birtaniya ya kaddamar da wani rahoton nazari a kwanan baya cewa, binciken kariyar cutar COVID-19 a jikin dan Adam ya nuna cewa, ya zuwa watan Febrairun shekarar 2022, yawancin yara Amurkawa ‘yan shekaru 17 da kuma kasa da 17 da haihuwa sun riga sun kamu da cutar ta COVID-19.
Daga watan Satumban shekarar 2021 zuwa watan Febrairun shekarar 2022, wata tawagar masu kimiyya karkashin shugabancin cibiyar dakilewa da kandagarkin cututtuka ta kasar Amurka ta gudanar da bincike kan kariyar cutar COVID-19 a jikin Amurkawa ‘yan kasa da shekaru 17 da haihuwa fiye da dubu 86, ciki hadda kananan yara 6100 ‘yan shekaru 1 zuwa 4 da haihuwa, a karshe tawagar ta yi hasashen yawan yara Amurkawa da ke da kariyar cutar COVID-19 a jiki sakamakon kamuwa da ita.
Sakamakon binciken ya nuna cewa, daga watan Disamban shekarar 2021 zuwa watan Febrairun shekarar 2022, yawan Amurkawa ‘yan shekaru 1 zuwa 4 a duniya ya karu fiye da sau daya, wato daga kashi 33 cikin kashi 100 zuwa kashi 68 cikin kashi 100.
Ya zuwa watan Febrairun shekarar 2022, a cikin yara Amurka ‘yan shekaru daban daban, yawan ‘yan shekaru 5 zuwa 11 da haihuwa da suka kamu da cutar COVID-19 ya kai matsayin koli, wato kaso 77 cikin dari, kana adadin ya kai kaso 74 cikin dari tsakanin ‘yan shekaru 12 zuwa 17 da haihuwa. Akwai bambanci a sassan Amurka dangane da shekarun yara na haihuwa, inda aka mayar da ‘yan shekaru sifiri zuwa 19 a matsayin yara a yawancin jihohin kasar.
Hukumar ilmin jinyar kananan yara ta kasar Amurka da kuma hukumar asibitocin kananan yara ta kasar sun kaddamar da rahoto a kwanan baya cewa, tun bayan barkewar cutar COVID-19 har zuwa yanzu, yara kusan miliyan 13 da dubu 300 sun kamu da cutar a Amurka.
Alkaluman da rahoton ya ambato, sun wuce zaton mutane kwarai da gaske. Amma wasu kwararru masu ruwa da tsaki sun yi nuni da cewa, binciken kariyar cuta a jikin dan Adam bai iya tabbatar da cewa, wani ya kamu da cutar sau daya ko sau da dama. Kana kuma yawan kariyar cutar yana raguwa sannu a hankali, don haka watakila ba a tanadi wasu cikin nazarin ba. (Tasallah Yuan)