logo

HAUSA

Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Ziyarci Lagos

2022-09-13 11:24:59 CMG Hausa

Daga ranar 7 zuwa 9 ga watan nan, jakadan kasar Sin a Tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya ziyarci jihar Lagos, inda ya gana da gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu.

Yayin ganawar tasu, Cui Jianchun ya ce, jihar Lagos tana kan gaba a Najeriya a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da kasuwanci da masana’antu, kuma wuri ne da baki Sinawa suka fara zuwa a Najeriya domin yin ciniki da kasuwanci a kasar.

Ya ce yankin yin ciniki cikin ‘yanci na Lekki, da masana’antar tace mai ta Dangote, da aikin tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki, wadanda kamfanoni masu jarin kasar Sin suka kafa suna cikin jihar ta Lagos, wadanda suke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2.

Kaza lika kasar Sin na son zurfafa hadin gwiwa a tsakaninta da jihar Lagos a sassa daban daban, musamman ma manyan ababen more rayuwa, da aikin sadarwa, masana’antu, zuba jari da cinikayya, karkashin tsarin manyan tsare-tsaren samun ci gaba da bunkasa na 5GIST tsakanin Sin da Najeriya.

A nasa bangaren, gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce, yankin ciniki cikin ‘yanci na Lekki yana bunkasa yadda ya kamata. Kuma ana dab da kammala kafa masana’antar tace mai ta Dangote, da aikin tashar jiragen ruwa mai zurfi ta Lekki. Kasar Sin ta bai wa jiharsa babban taimako a fannin samar da manyan ababen more rayuwa. Ya ce duk irin sakamakon da za a samu a babban zaben kasar a shekara mai zuwa, jihar ta Lagos za ta ci gaba da hada kai da kasar Sin, a kokarin kara azama kan aiwatar da karin ayyukan da za su amfani al’umma.  (Tasallah Yuan)