logo

HAUSA

Ruwa abokin aiki: Hadin-gwiwar Sin da Afirka na samar da alfanu ga rayuwar al’ummar Afirka

2022-09-13 14:15:52 CMG Hausa

Kwanza, shi ne sunan takardar kudin kasar Angola, wanda ya samo asali daga kogin Kwanza, kogi mafi girma da ake kira “mahaifiyar kogi” a kasar. Sanyawa takardar kudin kasar sunan wannan kogi, ya shaida muhimmacin dake tattare da ruwa ga al’ummar Angola. A ‘yan shekarun nan, sakamakon zuwan wasu ‘yan kasar China, kogin Kwanza, wanda ya taba rayuwar zuriyoyin al’ummar kasar Angola, ya sake inganta.

Allah ya horewa nahiyar Afirka dimbin albarkatun ruwa. Akwai wasu manyan koguna a nahiyar, ciki har da kogin Nilu, da kogin Kango, kana akwai hamadar Sahara mafi girma a duk duniya inda ke da karancin ruwa. A sassa da dama na nahiyar, a lokacin damina, babu na’urori na tarawa da adana ruwan sama, a lokacin rani kuma, a kan fuskanci bala’in fari.

A kasar Angola dake kudu maso yammacin nahiyar Afirka, akwai dimbin albarkatun ruwa amma ba’a kula da su yadda ya kamata, wannan ya sa take fuskantar matsalar rashin ruwa sosai. Allah ya huwacewa Angola koguna da dama, ciki har da kogin Kwanza da sauran wasu manyan koguna kimanin 30, amma yakin basasar da ya ki ci ya ki cinyewa, ya kawo babbar illa ga muhimman ababen more rayuwar al’umma dake kasar. Haka kuma, karancin kudade da rashin ci gaban fasahohi, su ma sun kawo cikas ga ayyukan rayawa gami da amfani da albarkatun ruwa, da hana ci gaban tattalin arziki da shafar rayuwar mazauna kasar.

A ’yan shekarun nan, kamfanonin kasar Sin da dama sun shiga kasar Angola, inda suke tafiyar da ayyukan da suka shafi gina tashoshin samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa, da ayyukan yaki da bala’in fari da na samar da ruwa da makamantansu.

Kogin Kwanza na da rassa da dama, inda a reshen tsakiyar sa, wani babban kamfanin kasar Sin mai suna Gezhouba ko kuma CGGC ke kokarin gina wata tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa mai suna Caculo Cabaca, wadda ita ce tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa maif girma da kamfanin kasar Sin ke ginawa a Angola. An kaddamar da aikin a watan Agustan shekara ta 2017, kuma har yanzu ana kan aikin gina ta.

Chen Yonggang shi ne manajan kula da aikin gina tashar Caculo Cabaca, inda ya ce, da zarar an gama aikin gina tashar, za ta iya biyan bukatun sama da kaso 40 bisa dari na al’ummar Angola a fannin wutar lantarki, kana, za’a iya rage fitar da kimanin ton miliyan 7.2 na iska mai gurbata muhalli a kowace shekara. Sa’annan, kudaden shiga da za’a samu daga aikin samar da wutar lantarkin, za’a yi amfani da su domin inganta sauran muhimman ababen more rayuwar al’umma, da hako ma’adinai, sa’annan za’a kara kyautata albarkatun ruwan kasar. Ban da wannan kuma, za’a samar da guraban ayyukan yi sama da dubu 6 ga mazauna wurin, da horas da wasu kwararrun kasar Angola a fannin gina tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa. Kamar yadda wani babban jami’in tashar dan kasar Angola ya ce, kamfanin China ya horas da su fasahohin gine-gine da yawa, al’amarin dake da matukar muhimmanci ga ci gaban Angola a nan gaba.

A watan Afrilun bana ne, aka fara amfani da ayyukan yaki da bala’in fari da wani kamfanin gine-gine na kasar Sin mai suna STECOL CORPORATION ya gina a jihar Cunene dake kasar Angola, wadanda suka kunshi wata babbar magudanar ruwa mai tsawon kilomita 150 da sauran wasu manyan na’urorin tattara ruwa.

Jihar Cunene tana kudancin kasar Angola, wadda ke makwabtaka da hamadar Namibiya. A wajen, kusan watanni 9 lokacin rani ne, inda a kan fuskanci matsanancin bala’in fari, kuma gonaki su kan kone, dabbobi ma kan mutu saboda kishirwa, sa’annan hakan na tilasta mazauna wurin da yawa su barin muhallansu zuwa kasashe makwabta. Amma yayin da aka fara gina ayyukan yaki da bala’in fari a wajen, magudanar ruwan da aka gina ta kai ruwa zuwa wuraren dake fama da matsalar fari, don yin ban ruwa ga gonaki, musamman a lokacin rani.

A nasa bangaren, babban manajan kamfanin kula da harkokin kudu maso yammacin Afirka na kamfanin STECOL CORPORATION, Zhao Yong ya bayyana cewa, da zarar ayyukan sun kammala, jama’a za su samu isasshen ruwan da yawansu ya zarce dubu 230 gami da dabbobi dubu 400 dake wajen. Haka kuma gwamnatin kasar Angola tana shirin kafa manyan gonaki a kewayen magudanar ruwan, don habaka ayyukan gona. A halin yanzu, idan ka je magudanar ruwan, za ka iya ganin dimbin shanu da tumakai dake shan ruwa, kana amfanin gona na girma yadda ya kamata.

A nasa bangaren, shugaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76, Abdulla Shahid ya ziyarci wajen a watan Mayun bana, inda ya yaba da cewa, a nan gaba, MDD za ta yi la’akari da tallata irin wannan salo zuwa sauran wasu yankuna da kasashe, wadanda ke fama da bala’in fari.

Tun da dadewa, ruwan sha mai tsafta na daya daga cikin matsalolin dake addabar kasar Angola, kuma karancin tsaftataccen ruwan sha na kara hadarin kamuwa da cutar amai da gudawa da kwalara da sauran cututtuka da ake dauka daga ruwa.

A watan Yunin bana, an kawo karshen aikin samar da ruwa na Cabinda da kamfanin China Railway 20th Bureau Group Corporation ya gina a Angola, kana an fara amfani da shi. A nasa bangaren, shugaban wannan kamfanin mai kula da harkokin Angola, Zhu Qihui ya ce, aikin shi ne aikin kyautata rayuwar dan Adam mafi girma a jihar Cabinda dake kasar Angola, wanda ya kunshi na’urorin da suka shafi adanawa da raba ruwa, wadanda ke iya samar da ruwan famfo a kowace rana ga kaso 92 bisa dari na al’ummar jihar Cabinda.

Akwai iyalai sama da 400 a yankin Futila dake jihar Cabinda, inda ake fama da matsalar karancin ruwan sha mai tsabta. A baya, na’urorin samar da ruwa dake wurin sun tsufa, har ma ba a amfani da su, wannan ya sa rayuwar mazauna wajen ke dogara kan wasu rijiyoyi kawai. Amma saboda karancin ruwan sama da ake yi a lokacin rani, ruwan dake cikin rijiyoyin ba zai iya biyan bukatun al’umma ba. Mazauna yankin Futila suna farin-cikin cewa, a halin yanzu, an shigo da bututun ruwa har gidajensu, abun da ya saukaka musu rayuwar yau da kullum. Inda suka mika godiya ga kamfanin kasar Sin, saboda gudummawarsa wajen samar da tsaftataccen ruwan famfo ga jama’ar Angola.

A nasa bangaren, ministan tattalin arziki da shirye-shirye na kasar Angola, Mario Augusto Caetano de Sousa ya bayyana cewa, matsalar da ke damun kasarsa, ita ce rashin amfani da albarkatun ruwa yadda ya kamata, ba matsalar karancin ruwa ba. Sakamakon kokarin da kamfanonin kasar Sin suka yi, yanzu halin yana kyautata. Kuma a ganinsa, kamfanonin kasar Sin sun kawo sabbin fasahohi da dabaru, wadanda suka taimaka sosai ga kyautata rayuwar mazauna wurin, gami da samar da ci gaba mai dorewa.

Tun lokacin da aka kafa kungiyar tarayyar Afirka wato AU a shekara ta 2002, har zuwa yanzu, kasar Sin da AU suna kara mu’amala da hadin-gwiwa tsakaninsu. Muhimman ababen more rayuwar al’umma da dama da aka yi a kasar Angola, ciki har da tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa mai suna Caculo Cabaca, da ayyukan yaki da bala’in fari dake jihar Cunene, da aikin samar da ruwa dake Cabinda, duk sun shaida hadin-gwiwa da zumunta tsakanin kasar Sin da kasar Angola da ma Afirka baki daya, da yanayi na cude-ni-in-cude-ka da aka yi na tsawon shekaru tsakanin Sin da Afirka.

Jakadan kasar Sin dake kasar Angola, Gong Tao, ya bayyana cewa, kasar Sin da kasar Angola, da ma sauran kasashen Afirka, duk da cewa suna da nisan gaske tsakaninsu, amma su aminai da ‘yan uwan juna ne. Sanin kowa ne cewa, ruwa da masu iya magana ke cewa, abokin aiki, yana kawo kyakkyawar makoma ga rayuwar bil-Adama baki, kuma muna fatan zai ci gaba da sada zumunta tsakanin Sin da Afirka. (Murtala Zhang)