logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da kungiyar malaman jami’o’in kasar gaban kuliya

2022-09-13 14:01:45 CMG Hausa

A jiya Litinin ne kotun ma’aikata a Najeriya ta dage sauraron karar da gwamnatin kasar ta gabatar gaban ta, inda take fatan kotun za ta umarci kungiyar malaman jami’o’in kasar ASUU ta janye yajin aikin da take yi. Kotun dai ta dage zaman sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan nan na Satumba.

Malaman jami’o’in Najeriya sun tsunduma yajin aiki ne tun daga ranar 14 ga watan Fabarairun farkon shekarar nan, inda suke neman gwamnati ta biya musu wasu bukatu, wadanda suka hada da inganta walwalar ma’aikata, da samar da karin kudaden gudanar da jami’o’in dake karkashin gwamnatin tarayya, da biyan alawus alawus na ma’aikata da na karin girma.

An gaza cimma nasarar warware sabani tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayyar Najeriya, a dukkanin zaman da aka gudanar tsakanin sassan biyu. A ranar Lahadi ne kuma, ministan ma’aikatar kwadagon kasar ya fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ya bayyana bukatar da gwamnatin Najeriyar ta gabatarwa kotu, ta umartar mambobin ASUU su koma bakin aiki, yayin da ake fatan ci gaba da gudanar da shawarwari, na warware takaddamar bisa tanadin doka.  (Saminu Alhassan)