logo

HAUSA

Wadda ta taba samun taimako tana taimakawa mutane yanzu

2022-09-13 08:18:51 CMG Hausa

 

Sunan yarinyar da ke cikin wannan hoto, shi ne Su Mingjuna, wadda aka haife ta a shekarar 1983 a iyalin manoma a gundumar Jinzhai a lardin Anhui. Iyayenta sun yi sana’o’i da dama da suka hada da kamun kifi, kiwon alade, shuke-shuke da dai sauransu, amma ba su samu kudi da yawa ba. A shekarar 1991, mai daukar hoto ya ziyarci Jinzhai. Su Mingjuan ta yi karatu a kan tebur. Muhallin koyar da yara a wurin da kuma yadda yara suke karatu tukuru sun girgiza mai daukar hoton. Ya dauki hoton Su Mingjuan. Hoton Su Mingjuna ya ja hankalin mutane sosai, kuma ya zama alamar babban aikin taimakawa yara su koma karatu a wurare masu talauci a kasar Sin. Yara masu yawa sun koma karatu bisa taimakon sassa daban daban. Su Mingjuna ta kammala karatu a jami’a ba tare da wata matsala ba bisa taimakon masu kirki, yanzu tana aiki a banki, ba ta manta da taimakon da ta taba samu ba, tana kokarin taimakawa wadanda ke bukatar taimako. (Tasallah Yuan)