logo

HAUSA

Amurka Mai Matukar Son Leken Asiri A Duniya

2022-09-12 15:30:26 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, kwanan baya an kutse a kwamfutocin jami’ar masana’antu ta arewa maso yammacin kasar Sin, wannan jami’a na da kwararru da masana da kimiyya a fannin tsaro. Bincike ya nuna cewa, hukumar tsaron kasar Amurka (NSA) ce ta aika wannan laifi, wadda ta kan yin korafi game da leken asiri. Yau “duniya a zanen MINA” na bayyani kan yadda Amurka take leken asiri a duniya ba tare da jin kunya ba.

Ban da kutse a yanar gizon wannan jami’a da muka ambata, Amurka ta kan yi leken asiri kan hukumomi da jami’o’i da daidaikun mutane a kasar Sin. Abin tsoro ma shi ne, watakila irin wannan kutse da Amurka ta kan yi kan ko wane mutum a duniya. Lokacin da ka mutum yake waya da abokansa, ko sakwanin da aka wallafa a kan Intanet da kuma wasu muhimman bayanai, dukkansu ba sirri ba ne ga NSA.

Kama daga batun leken asiri na PRISM har zuwa kutsen da aka yiwa jami’ar kasar Sin a wannan karo, dukkansu na shaida cewa, Amurka tana matukar son yin leken asirin saura ta kowa ce fuska. Don haka, ya kamata mu kiyaye muhimman bayanan sirrinmu, da ikon mallakar fasaha na hukumomi da kuma ‘yancin kare sirrin mutum. Amma matakan da Amurka ke dauka, na kawo babbar illar ga wadannan hakkoki na al’ummar sauran kasashe. Ya kamata, ‘yan siyasar Amurka su bude ido da kunnuwansu, su fahimci mawuyancin halin da al’ummar kasarsu ke fuskanta, a maimakon zama wani kifin teku mai kafa takwas don leken asirin duniya. (Mai zana hoto kuna mai rubuta sharhi:MINA)