logo

HAUSA

Rashin Yarda Da Kai Ya Sa Wasu Kasashen Yamma Ke Neman Ta Da Matsaloli

2022-09-12 21:33:11 CMG Hausa

Ofishin babban kwamishina mai kula da aikin kare hakkin dan Adam na MDD ya gabatar da wani rahoto dangane da jihar Xijiang ta kasar Sin a kwanan baya, wanda ya nuna al’adar kasar Amurka da wasu kawayenta ta neman yin amfani da batun hakkin dan Adam a matsayin wani makami.

Me ya sa a ce haka?

Saboda da farko dai, yadda aka tsara rahoton ya saba ka’idoji. A matsayinsa na daya daga cikin hukumomin MDD, ya kamata ofishin babban kwamishina mai kula da hakkin dan Adam ya gudanar da duk wani aiki ne bisa iznin da majalisar kare hakkin dan Adam ta ba shi, kuma ba tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata kasa ba. Amma ofishin ya gabatar da wannan rahoto kai tsaye, ba tare da neman samun izini ba, kuma bai taba neman sauraron ra’ayin Sin ba. Kana ta wannan hanya ya tsoma baki cikin harkokin gida na kasar Sin.

Na biyu, shi ne bayanan dake cikin rahoton sun saba da sanarwar da Madam Veronica Bachelet, babbar kwamishinar mai kula da aikin kare hakkin dan Adam ta MDD, ta gabatar, a ranar 28 ga watan Mayun bana, bayan da ta kammala ziyararta a jihar Xinjiang ta kasar Sin. Inda ta yaba da kasar Sin, kan kokarinta a fannonin rage talauci, da kare mutane marasa karfi, da yunkurin tabbatar da ingancin hakkin dan Adam, da dai sauransu.

Hakika idan mun yi nazari kan mutanen da suke aiki a ofishin babban kwamishina mai kula da aikin hakkin dan Adam, za a fahimci cewa, zai yi wahala wannan ofishi ya gabatar da wani rahoto na gaskiya. Saboda kasar Amurka da wasu kawayenta sun tura ‘yan korensu don su zama manyan jami’an ofishin, inda su kan yin amfani da wasu bayanai marasa gaskiya wajen tsara rahotannin da suke haifar da matsin lamba ga kasar Sin, da sauran kasashe masu tasowa.

Amma me ya sa kasar Amurka da abokanta ke kokarin yin amfani da damammaki daban daban wajen shafa kashin kaza ga kasar Sin, da kafa shingaye ga sauran kasashen masu tasowa? A ganina, suna haka ne domin ba su yarda da kansu ba.

Kasashen yammacin duniya na ganin cewa, dole ne kasashe masu tasowa su bi tsarin dimokuradiya irin nasu, da zama karkashin jagorancinsu, kafin su iya samun ci gaba mai dorewa. Sai dai kasar Sin, a karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta zabi hanyar da ta tsara da kanta kuma da dace da yanayin al’ummarta, inda ta dauki tsarin gurguzu mai siffar musamman ta Sin, tare da samun babban ci gaba, cikin gomman shekarun da suka wuce. Wannan ya sa kasashen yamma kaduwa, saboda yadda kasar Sin ta samu nasara ta nuna cewa, kasashe masu tasowa za su iya raya kansu, ta hanyar musamman da suka zaba, maimakon ci gaba da bin umarnin kasashen yamma.

Wannan damuwa ta sa kasar Amurka da wasu kawayenta ke kokarin gogayya da kasar Sin, da haifar da matsaloli a harkoki masu alaka da hakkin dan Adam, da jihar Xinjiang, da yankin Taiwan na kasar Sin, da dai sauransu, don hana kasar Sin samun ci gaba. Sai dai kasar Sin ta yi ta samun nasarar daidaita wadannan matsaloli, bisa cikakken imanin da take da shi a kan turbar da ta zaba. Haka kuma Sinawa suna iya hakuri da mabambantan ra’ayoyin da ake samu a duniya, da iya tinkarar duk wani kalubalen da suka kunno kai yayin da suke kokarin raya kasarsu.

A nasu bangare, kasashe masu tasowa su ma sun fara ganin yanayin rashin adalci na tsare-tsaren kula da harkokin duniya da kasashen yamma suka gabatar, wannan ya sa suke kokarin nemo hanyar raya kansu wadda ta dace da yanayin da suke ciki. Wannan wani muhimmin yanayi ne da muke fuskanta a wannan zamanin da muke ciki. (Bello Wang)