logo

HAUSA

Ministan Najeriya ya yi maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar

2022-09-12 15:39:48 CMG Hausa

Tarayyar Najeniya, babbar kasuwa ce da kasar Sin take zuba jari, da gudanar da cinikayya, da fitar da kayayyaki, da kuma ayyukan gine-gine a nahiyar Afirka. Kwanan baya ministan masana’antu da cinikayya da zuba jari na tarayyar Najeriya Otunba Adebayo ya bayyana yayin da ya zanta da wakilin CMG cewa, Najeriya da Sin suna gudanar da hadin gwiwar kut-da-kut a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar al’umma da tattalin arziki da cinikayya, kuma Najeriya tana maraba da kamfanonin kasar Sin da su zuba jari tare kuma da kafa kamfanoni a kasar, kana tana fatan za ta yi amfani da damar shiga bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa daga ketare na kasa da kasa na kasar Sin karo na 5 da za a shirya a bana, domin tallata kayayyakin Najeriya ga masu sayayya na kasar Sin.

Rahotanni sun nuna cewa, gaba daya jimillar darajar cinikayyar dake tsakanin kasar Sin da tarayyar Najeriya a shekarar 2021, ta kai dalar Amurka biliyan 25.68, adadin da ya karu da kaso 33.3 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

Game da halin da ake ciki a bangaren hadin gwiwar dake tsakanin Najeriya da Sin a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar al’umma da tattalin arziki da cinikayya da zuba jari kuwa, minista Adebayo yana mai cewa, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekarar 1971, dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu ta bunkasa daga dukkan fannoni, kuma nan gaba ana sa ran za a ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin Najeriya da Sin zuwa wani sabon matsayi. (Jamila)