logo

HAUSA

An kammala gasar bidiyo ta matasan Sin da Afrika ta “Great to Meet You”

2022-09-11 16:02:12 CMG Hausa

An kammala gasar bidiyo ta matasan Sin da Afrika ta “Great to Meet You” karo na farko jiya Asabar, gaba daya bidiyo 102 ne suka shiga gasar, inda guda 3 suka samu kyautar matsayi na farko, guda 6 suka samu na biyu, saura goma suka samu na matsayi na uku.

An shirya bikin mika lambobin ne a hedkwatar babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG na nahiyar Afirka dake birnin Nairobin kasar Kenya, tare kuma da gabatar da shirye-shirye kai tsaye ta kafar bidiyo a fadin duniya.

Hedkwatar CMG dake Afirka ce ta shirya gasar tare da hadin gwiwar makarantar koyon aikin yada labarai da al'adun kasa da kasa na jami'ar Zhejiang, inda suka gayyaci shugabannin manyan kafofin watsa labarai na kasashen Afirka da masanan kafofin watsa labarai na kasar Sin domin su tantance bidiyon da aka gabatar.

Babban taken gasar shi ne “Matasan Sin da Afirka su hada kai domin gina kyakkyawar makomar al’ummomin Sin da Afirka a sabon zamanin da muke ciki”, ana sa ran matasan Sin da Afirka, za su nuna makoma mai kyau ta hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu ta hanyar daukar faifan bidiyo.

Tun bayan da aka kaddamar da gasar a ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata, matasan Sin da Afirka wadanda suke tsakanin shekaru 20 zuwa 40 sun nuna kwazo da himma wajen gabatar da faifan bidiyon da suka dauka, daga kasashen Najeriya da Kenya da Benin da Angola da Tanzaniya da Jibouti da Kamaru da Madagascar da Mauritius da Mozambick da sauransu. (Jamila)