logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa mai tsanani ta yi barna a Sudan ta kudu

2022-09-11 16:11:06 CMG Hausa

A ranar 9 ga watan Satumba, gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta ayyana yankunan kasar da ambaliyar ruwa ta shafa, a matsayin yankin bala'i na kasa.

Ministan yada labaran kasar Michael Makuei Lueth ya ce, ambaliyar ta raba dubban mutane da muhallansu a kasar tare da halaka daruruwan mutane. Kwanan baya ne, shugaban kasar Salva Kiir Mayardit ya yi kira ga abokan huldar jin kai, da su agazawa kasar.

Rahotanni sun nuna cewa, kasar Sudan ta kudu ta fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani a cikin shekaru uku da suka gabata, a shekarar bara ta 2021 ma, ambaliyar ruwa ta shafi al’ummun kasar da yawansu ya kai sama da dubu 800. (Jamila)