logo

HAUSA

Tattalin arzikin Nijeriya ya samu tagomashi duk da kalubalen da ake fuskanta

2022-09-10 15:53:47 CMG Hausa

 

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce tattalin arzikin kasar na ci gaba da nuna juriya, kuma yana samun tagomashi, duk da kalubalen da yake fuskanta.

Shugaban ya bayyana haka ne a jiya, yayin kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan raya tattalin arzikin a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, inda ya ce asarar man fetur mai yawa wanda shi ne kashin bayan tattalin arzikin kasar, da annobar COVID-19 da rikicin Rasha da Ukraine, sun haifar da mummunan tasiri kan tattalin arzikin kasar mafi yawan al’umma a Afrika.

Ya ce yayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar kalubale da dama da ya hada da matakan kulle saboda annobar COVID-19 da tsaikon samar da kayayyaki da hauhawar farashinsu a duniya, tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da nuna juriya da samun tagomashi, duk tasirin karuwar kudin musayar dala da na kudin ruwa a fadin duniya.

Shugaban ya kuma bukaci kwamitin da ya yi tunani mai zurfi domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta a Nijeriya. (Fa’iza Mustapha)