logo

HAUSA

'Yan sama jannati na Shenzhou-14 sun yi 'Tattaunawar Tiangong' tare da matasan Afirka

2022-09-12 20:55:05 CRI

Kwanan baya, matasa daga kasashen Afirka 8 da suka hada da Najeriya, da Habasha, da Masar da dai sauransu, sun gudanar da taron "Tattaunawar Tiangong", wato tashar nazarin sararin samaniya ta kasar Sin tare da 'yan sama jannatin Shenzhou-14, wadanda har yanzu suke gudanar da ayyuka a tashar sararin samaniyar kasar Sin ta kafar bidiyo, inda suka yi mu'amala a tsakaninsu mai armashi da kuma nishadantarwa.

Wannan aiki mai taken "Tattaunawar Tiangong- Tambayoyi da Amsoshi tsakanin Ma'aikatan ‘Yan Sama Jannati na Shenzhou 14 da Matasan Afirka", an gudanar da shi ne karkashin shugabancin hukumar Tarayyar Afirka, da tawagar kasar Sin a Tarayyar Afirka, da ofishin ayyukan kumbon da ke daukar 'yan sama jannati na kasar Sin. Ban da babban wurin da aka kebe a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka wato AU dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, an kuma kebe wasu wuraren tattaunawa a kasashen Afirka guda 8, wadanda suka hada da Najeriya, da Algeria, da Masar, da Habasha, da Namibiya, da Senegal, da Somaliya da Afirka ta Kudu da dai sauransu. Matasa daga kasashen Afirka fiye da 50 da kusan mutane 1,000 daga sassa daban-daban na kasar Sin da Afirka sun halarci taron.

Wakilan matasa daga wuraren 8 sun gabatar da tambayoyi, irin su ko ana iya ganin Hamadar Sahara, da Dutsen Kilimanjaro daga kan tashar sararin samaniyar kasar Sin? Yaya mata 'yan sama jannati suka tabbatar da mafarkinsu? Yaya ake gudanar da zaman rayuwa da wasu ayyukan nishadi a sararin samaniya bisa hali na rashin nauyi? Wadanne ayyuka 'yan sama jannatin suke yi? Kuma wadanne halaye ne dole 'yan sama jannati nagari su mallaka, da dai sauransu?

A wurin da aka kebe a Najeriya, wakilai da dama na daliban makarantun gaba da sakandare, sun saurari hirarraki tsakanin matasan Afirka da 'yan sama jannati, sun kuma koka da sihirin sararin samaniya, da girman sararin samaniya, sun kuma nuna mamaki kan yadda fasahar sararin samaniyar kasar Sin ta samu ci gaba, da kuma kyawun 'yan sama jannatin kasar Sin.

Leon Onunaiju, dalibi dan Najeriya mai shekaru 14 a makarantar sakandare, yana daya daga cikin wakilan matasa daga kasashen Afirka takwas, da suka yi wa 'yan sama jannatin kasar Sin tambayoyi. Ya shaida wa wakilinmu cewa, "Tattaunawar Tiangong" ta sa ya samu kwarin gwiwa sosai, kuma ya koyi ilmin sararin samaniya masu yawa. Ya ce,

“Muna godiya ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a fannin binciken sararin samaniya, yanzu za mu iya kara habaka wannan hadin gwiwa, ta yadda za a iya tura karin 'yan Afirka, ciki har da 'yan Najeriya zuwa sararin samaniya. Ina fatan nan gaba, za mu iya yin hadin gwiwa ba kawai a sararin samaniya ba, har ma a wasu fannoni daban-daban, kamar yadda a kan ce, tafiyar mil dubu na farawa ne da taku guda, wannan mataki zai kara habaka, har a nan gaba, ya zama matakai da yawa na ci gaban Sin da Afirka baki daya.”

'Yan sama jannatin kasar Sin guda uku da suka hada da Chen Dong, da Liu Yang, da Cai Xuzhe, da ke gudanar da ayyuka a tashar sararin samaniya ta Tiangong, sun yi tattaunawa da matasan Afirka, inda suka amsa tambayoyinsu game da rayuwar sararin samaniya, da gwaje-gwajen kimiyya, da yadda ake horar da 'yan sama jannati da dai sauransu. Wata yariniya ‘yar shekaru 16 mai suna Danielle Chisom, daliba a reshen Najeriya, ta ce,

“Ina ga bikin na yau ya yi kyau sosai, muna da ajin kimiyya a makaranta, kuma ina fata in zama ‘yar sama jannati idan na girma, wannan tattaunawar ta amsa tambayoyi da yawa da nake so in sani.”

Michelle Okapor, 'yar Najeriya mai shekaru 14, dalibar makarantar sakandare, ta yi imanin cewa, aikin "Tattaunawar Tiangong" yana iya ingiza kirkire-kirkire. Ta ce,

"Bikin na yau, ya amsa tambayoyi da yawa da suka shige min duhu, kuma a gani na wannan aiki ne mai kyau na kirkire-kirkire, yana kasancewa mai ingiza kirkira."

'Yan sama jannatin kasar Sin uku, Chen Dong, da Liu Yang, da Cai Xuzhe, sun amsa tambayoyin daliban daya bayan daya. Amsoshinsu masu ban sha'awa kuma cike da ilmi, sun bayar da mamaki da tunanin matasan Afirka. 'Yan sama jannatin sun karfafa wa matasa gwiwa da cewa, "hanyar zuwa sararin samaniya tana farawa da kafafuwansu", kuma suna fatan za su yi karatu tukuru don samun fasahohi, da kuma jajircewa wajen binciken gabobin sararin samaniya.

Mataimakin darektan ofishin ayyukan kumbon da ke daukar 'yan sama jannati na kasar Sin Lin Xiqiang, ya gabatar da aikin raya sararin samaniya na kasar Sin, da bayani kan tashar sararin samaniya ta "Tiangong". Ya ce, tashar "Tiangong" ta kasar Sin ce da ma duniya baki daya, kuma wani dandali ne budadde ga ayyukan binciken sararin samaniya, da gudanar da nazarin kimiyya, kana yana maraba da matasan Afirka da za su tashi tare da 'yan sama jannatin kasar Sin, a tashar sararin samaniyar kasar Sin a nan gaba don gudanar da ayyuka tare.

A cikin jawabinsa, jakadan kasar Sin a kungiyar tarayyar Afirka Hu Changchun, ya bayyana cewa, Sin da Afirka suna da buri daya, na yin bincike a sararin samaniya, kuma wannan bikin ya nuna hadin kai a tsakanin Sin da Afirka. Har ila yau, ya nuna fatan da Sin da Afirka ke da shi, na hada karfi don hawa matsayi na kololuwar kimiyya da fasaha.

An ce, wannan aiki na "Tattaunawar Tiangong - Tambayoyi da Amsoshi tsakanin 'yan sama jannatin Shenzhou-14 da matasan Afirka" na daya daga cikin bukukuwan murnar cika shekaru 20, da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Tarayyar Afirka. Shi ne kuma karo na farko, da wata babbar kasa a fannin sararin samaniya, ta shirya wani aiki na yin mu’ammala a tsakanin ‘yan sama jannatin dake sararin samaniya da matasan Afirka.