Cinikin Waje Na Kasar Sin Shi Ne Jigon Tattalin Arzikin Duniya
2022-09-08 20:22:59 CMG Hausa
A cewar alkaluman kididdigar da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar jiya Laraba, jimillar darajar shigi da ficin kayayyaki na kasar Sin a watanni 8 na farkon bana, ta kai kudin Sin yuan triliyan 27.3, wanda ya karu da kashi 10.1 cikin 100 bisa makamacin na shekarar 2021. Daga cikin su, fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, ya karu da kashi 14.2 bisa 100, sannan fannin shigo da kayayyaki, ya karu da kaso 5.2 cikin 100.
Yayin da kasar Sin take fuskantar koma bayan ci gaban tattalin arzikin duniya da raguwar bukatar kayayyaki a ketare, bunkasuwar cinikayyar waje da kasar Sin ta samu a cikin watanni 8 na farkon bana, ba ta zo mata cikin sauki ba, wadda ke nuna halaye na musamman na kuzari da tsayin daka mai gamsarwa.
A yau ne kuma, aka gudanar da bikin baje kolin zuba jari da cinikayya na kasa da kasa na kasar Sin karo na 22 (CIFIT) a lardin Fujian dake yankin kudu maso gabashin kasar Sin. 'Yan kasuwa daga kasashe da yankuna kimanin 70 ne suka halarci bikin ko dai ta yanar gizo ko a zahiri. Wannan wani dandali ne na daban da kasar Sin ta samar wa duniya don bunkasa cinikayya da zuba jari a duniya. A kullum karfin cinikin ketare na kasar Sin, ya kasance tamkar wani "tafkin ruwa mai gudana " dake bunkasa tattalin arzikin duniya.(Ibrahim)