logo

HAUSA

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Riba Ce Ga Kasashe Masu Tasowa

2022-09-08 18:32:34 CMG Hausa

Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da nazari, da fafutukar neman kyakkyawar makoma a wannan mawuyacin lokaci da duniya take ciki, musamman ta fuskar koma bayan tattalin arziki, da gurguncewar sassa daban daban na ci gaba, sakamakon bullar annobar COVID-19, da rikicin kasar Ukraine da suka haifar da mummunar illa ga duniya, a hannu guda, kasashe musamman masu tasowa, na da kyakkyawan fatan samun ci gaba da wadata, karkashin ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa, bisa shawarar nan ta “Ziri Daya da Hanya Daya” wadda kasar Sin ta gabatarwa duniya.

Cikin irin wadannan ayyuka da a yanzu haka ke daf da kammala, akwai ginin tashar teku mai zurfi ta yankin Lekki na jihar Lagos dake kudu maso yammacin Najeriya, wadda kasar Sin ta tallafa wajen gudanarwa.

’Yan Najeriya da dama, da masana tattalin arziki a kasar, na jinjinawa kasar Sin, bisa aiwatar da wannan muhimmin aiki mai tarin alfanu, wanda zai fadada damar Najeriya ta karbar manyan jiragen dakon kayayyaki daga sassan duniya daban daban.

Aikin wanda zai lashe tsabar kudi har dalar Amurka biliyan 1.5, a yanzu ya kai kaso 95 bisa dari na kammala, ana kuma sa ran gama shi baki daya zuwa karshen shekarar nan ta 2022. Tashar za ta hade da yankin ciniki cikin ’yanci na jihar ta Lagos.

Da zarar tashar ta kammala, za ta zamo ta 3 da Najeriya ke da su, baya ga tsoffin tashoshin ruwa masu karbar jiragen ruwa guda biyu dake fama da cinkoso. Sabanin tsofannin tashoshin biyu, sabuwar tashar teku mai zurfi ta Lekki, za ta iya karbar kayan da yawansu zai kai na sama da manyan sundukan dakon kaya masu fadin kafa 20 har miliyan 2.7 a duk shekara, kana tashar tekun mai zurfi, za ta samarwa Najeriya zarafin karbar sundukan dakon kayayyaki daga 3,000 zuwa 20,000 a kullum, wanda hakan ya sanya tashar zama daya daga ayyuka mafi muhimmanci da Najeriya za ta ci gajiyar su, karkashin shawarar “Ziri Daya da hanya Daya”.

Ko shakka babu wannan muhimmin aiki ne da zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta fuskar samun karin haraji, da guraben ayyukan yi, da fadada damammaki na kasuwanci da cinikayya, baya ga rage tsadar kudaden fito, da kara zamanintar da salon ba da hidimomin shige da fice da tashar za ta yi a kasa irin Najeriya, wadda ita ce mafi girman tattalin arziki a nahiyar Afirka. (Saminu Hassan)