logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 10 a jihar Bauchi

2022-09-08 13:57:01 CMG HAUSA

 

A kalla mutane 10 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku biyo bayan mamakon ruwan sama a jihar Bauchi dake arewacin Najeriya,

sannan 19 daga cikin dukkan kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi suna fama da bala’in ambaliyar.

Mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya reshen jihar, Adams Nayola ne ya fadi haka, ya kuma ce, an riga an tabbatar da ganin yankunan kananan hukumomi 12 sun fuskanci mummunan asara, kuma har yanzu, hukumar ceto na kokarin tara bayanan asarar da ambaliyuar ta haddasa.

Kananan hukumomin jihar sun bayyana cewa, tun daga karshen watan Agusta, ake ta sheka ruwan sama kamar bakin kwaya.

Adams Nayola ya kara da cewa, dubban mazauna suna samun mafaka a wurare daban-daban, kuma ambaliyar ta katse wasu al’ummomi. (Amina Xu)