logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su yi kokarin hana bala'in jin kai a Somaliya

2022-09-08 13:57:12 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Dai Bing, ya bayyana a gun taron kwamitin sulhu na MDD game da batun Somaliya karo na 7, cewa, wajibi ne kasashen duniya su gaggauta daukar matakan jin kai, da kara ba da taimako, da daukar matakan hana afkuwar bala'in jin kai a Somaliya.

Dai Bing ya kara da cewa, halin da ake ciki na jin kai a kasar Somaliya a halin yanzu yana da matukar muni, matsalar fari da ke ci gaba da shafar rayuwar kusan rabin al'ummar kasar, karancin abinci na kara tabarbarewa cikin sauri, kuma hadarin yunwa da rashin abinci mai gina jiki ya kara tsananta. Kasar Sin ta yi maraba da nadin manzo na musamman don tunkarar fari da shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed ya yi, da nufin gudanar da ayyukan jin kai yadda ake bukata. Kana tana goyon bayan MDD wajen samar da kason gaggawa ga kasar Somaliya da sauran kasashen dake yankin kahon Afirka, a kokarin da ake na kawar da matsalar fari.

Dangane da batun tsaro a Somaliya kuwa, Dai Bing ya ce, kasar Sin tana goyon bayan shugaba Mahmoud wajen daukar matakan yaki da ta'addanci da matakin gaggauta na sake tsara sojoji a matsayin muhimman ayyuka a lokacin mulkinsa. Tana kuma maraba da  yadda gwamnatin Somaliya ta karfafa hadin gwiwa da manyan abokan huldar kasa da kasa, ciki har da kungiyar Tarayyar Afirka, da sa kaimi ga aiwatar da shirin kasar na mika mulki na wucin gadi, da daukar nauyin kiyaye tsaron kasa sannu a hankali. Baya ga haka, kasar Sin ta yi kira ga manyan bangarori masu samar da tallafi, da su samar da dauwamammen hanyoyin samun kudade ga tawagar wanzar da zaman lafiya ta AU a Somaliya, domin tabbatar da cewa dakarun tawagar sun samu isassun alawus yadda ya kamata. (Mai fassara: Bilkisu Xin)