logo

HAUSA

Jarirai fiye da dubu 124 sun mutu a Najeirya sakamakon ciwon gudawa

2022-09-08 13:46:51 CMG HAUSA

 

Jaridar The Punch da ake bugawa a Najeriya, ta ba da labari a jiya Laraba cewa, ministar harkokin jin kai, da bala’o’i da ci gaban jama’a ta Najeriya Hajiya Sadiya Farouk, ta ziyarci sansanin ’yan gudun hijirar Bakassi da ke jihar Cross Rivers, inda ta nuna cewa, a kalla jarirai dubu 124 ’yan kasa da shekaru 5 a duniya, suke mutuwa sakamakon gudawa da sauran cututtuka dake da nasaba da kwayoyin cuta da ake dauka daga bayan gida. Ta kuma ce a kalla mutane miliyan 47 a Najeriya, na ci gaba da yin bahaya a fili sakamakon rashin isassun bayan gida, abin da ya baiwa kwayoyin cutar shan inna da kwalara da ciwon hanta da sauran annoba ta hanyar yaduwa cikin sauri. Don haka, ta yi kira ga ’yan gudun hijira, da su daina yin bahaya a fili don gujewa yaduwar cututtuka. (Amina Xu)