Al’ummar Ghana sun yi farin ciki da ganin kofin kwallon kafa na duniya
2022-09-08 18:37:15 CMG Hausa
Daruruwan al’ummar kasar Ghana, sun yi dafifi a filin wasan kwallon gora ko Polo dake birnin Accra a ranar Lahadi, domin ganewa idanun su kofin kwallon kafar duniya da hukumar FIFA ta kai kasar, a wani bangare na ran gadi da FIFA ke yi da kofin, domin masu sha’awar wasan kwallo.
‘Yan kallon sun rika shewa da tafi, suna daukar hotunan kofin cikin nishadi. A cewar Isaac Addo, wani mai sha’awar kwallon kafa, "Na cika da farin cikin ganin wannan kofi kai tsaye ido da ido, ina fatan kofin zai dawo kasar Ghana". Shi ma Emelda Nutifafa, mai sha’awar kwallon kafa, cewa ya yi abun farin ciki ne ganin yadda wannan kofi na gasar kwallon kafar duniya ya isa Ghana.
A ranar Asabar ne hukumar FIFA ta kai kofin kasar Ghana, inda zai kasance a kasar tsawon yini biyu. Kofin ya samu rakiyar tauraron dan kwallon kasar Faransa David Trezeguet.
Da yake tsokaci game da zuwan kofin na duniya kasar Ghana, shugaban hukumar kwallon kafar kasar GFA Kurt Okraku, ya bayyana yayin wata tattaunawa da manema labarai cewa, ya gamsu da matakin, yana mai cewa "Na yi matukar jin karsashi da karfin gwiwa, kuma a gani na hakan zai karfafa gwiwar tawagar kwallon kafar mu”.
Kasar Ghana na cikin kasashen Afirka 5, da za su buga gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 a kasar Qatar, a watannin Nuwamba zuwa Disamba.
Baya ga kasar Ghana, sauran kasashen Afirka da za su wakilci nahiyar Afirka a gasar ta karshen shekarar bana, su ne Kamaru, da Senegal, da Morocco, da Tunisia.
Ghana ta doke Najeriya a wasan neman gurbin buga gasar cin kofin CHAN
Kungiyar kwallon kafar Ghana, ta doke takwararta ta Najeriya da ci 2-0, a wasan farko na rukunin su, yayin da kasashen ke kokarin samun gurbin buga gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka ko CHAN, a wasan da aka buga a birnin Cape Coast na bakin ruwa.
Kungiyar Ghana ta lashe maki 3, duk da kokarin da Najeriya ta yi na samun nasara a wasan. An kammala zangon farko na wasan ba wadda ta yi nasara, sai bayan hutun rabin lokaci ne Ghana ta yi nasarar jefa kwallo a ragar Najeriya, ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 49.
Kafin a tashi wasan ne kuma a na minti na 85, dan wasan Ghana Seidu Suraj ya kara kwallo ta biyu a ragar Najeriya. Yanzu kuma zagaye na biyu na wasan kasashen biyu zai gudana ne a birnin Lagos na kudancin Najeriya, inda kungiyar da ta yi nasara tsakanin su za ta shiga jerin masu buga gasar nahiyar ta Afirka ko CHAN, wanda za a buga a shekarar 2023 dake tafe a kasar Aljeriya.
Karo 3 ke nan a jere, kasar Ghana ba ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin na CHAN ba.
Harbe harben da suka auku a filin wasan kwallon kafa a Mexico ya sabbaba kisan mutane 4
Rahotanni na cewa, a kalla mutane 4 sun rasu, ciki har da tsohon magajin gari, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta yayin wani wasan kwallon kafa a garin Yecapixtla na jihar Morelos, dake tsakiyar kasar Mexico. Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun bude wuta a filin wasan ne da yammacin ranar Juma’a, da misalin kafar 9:15 daidai da 02:15 agogon GMT.
Cikin wadanda suka rasu, har da tsohon magajin garin Yecapixtla, Refugio Amaro Luna, da wasu karin mutane 2, bayan an garzaya da su asibiti. Kaza lika akwai wasu mutanen 10 da suka ji raunuka yayin harbe harben. Ana samun karin aukuwar laifuka a garin Morelos, garin da ya zamo kan gaba a garkuwa da mutane a duk fadin kasar Mexico, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta bayyana.
An bayyana sunayen ‘yan wasan da za su wakilci kasar Uganda a gasar Rugby ta 2022
Babban kocin kungiyar Rugby ta kasar Uganda Tolbert Onyango, ya sanar da ‘yan tawagar kungiyar sa ta “Rugby Sevens” mai kunshe da ‘yan wasa 12, wadanda za su buga gasar Rugby ta duniya ta 2022 da za a yi a birnin Cape Town na Afirka ta kudu, tsakanin ranakun 9 zuwa 11 ga watan Satumbar nan.
Kocin ya ayyana Michael Wokorach, da Ian Munyani a matsayin wadanda za su jagoranci tawagar ‘yan wasan, yayin da Adrian Kasito, da Timothy Kisiga, da Phillip Wokorach, za su kasance cikin ‘yan wasan da za su halarci gasar a karo na 2.
Koci Onyango ya ce "Mun san girman matsayin gasar cin kofin duniya ta Rugby, kuma ‘yan wasan mu sun shirya sosai, sun buga gasanni masu yawa, yayin da suke shirin buga wannan muhimmiyar gasa. Ina fatan nasarar da muka samu a gasannin baya na kasashe renon Ingila, da na duniya da aka gudanar a birnin Santiago, za su ba mu kwarin gwiwar taka rawar gani a wannan gasa dake tafe”.
Uganda ta samu gurbin shiga gasar dake tafe ne, bayan ta lashe gasar nahiyar Afirka ta “Africa Rugby Sevens”. Tawagar za ta fafata a gasar dake tafe a rukunin C tare da kasashen Jamus, da Uruguay da Lithuania. Wannan ne kuma karo na 2 da kungiyar za ta halarci gasar cin kofin duniya na Rugby, bayan da ta buga gasar a shekarar 2018, a birnin San Francisco na Amurka, ta kuma zo matsayi na 19 a wancan karon.