logo

HAUSA

Yadda baje kolin CIFTIS da na mutum-mutumin inji za su habaka tattalin arzikin Sin da duniya baki daya

2022-09-07 09:42:42 CMG Hausa

An kammala bikin baje kolin cinikayyar hidima na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2022 da aka shafe kwanaki 6 ana gudanarwa ranar Litinin. Yayin bikin na bana, an gudanar da jigon taruka 128 da gabatarwa da shawarwari guda 65, wanda ya kai ga cimma jimillar nau’o’in sakamako guda 1,333 da suka hada da hada-hadar kasuwanci,da zuba jari, da gabatar da yarjeniyoyi da dabarun hannayen jarin kirkire-kirkire da dai sauransu. Yayin da yawan mahalarta taron ya zarce 250,000.

Bikin baje kolin CIFTIS na wannan shekara, ya kasance mafi girma a ma'auni da kuma kimar habaka kasashen duniya. bikin baje kolin, ya jawo hankalin manyan kamfanoni 507 dake kan gaba a duniya don halartar bikin a zahiri, yayin da a karon farko aka gabatarwa kamfanoni da cibiyoyi da sabbin samfura fiye da 100, da sabbin fasahohi da nasarori a fannonin kwaikwayon tunanin dan-Adam.

Bugu da kari, an sanya sabuwar rukunin kungiyar ciniki ta Global Service Trade Alliance, a matsayin kungiyar hadin gwiwa ta kasa da kasa, kana an gudanar da taron 'yan kasuwa masu samar da ayyukan hidima na duniya. A karon farko kasashe 10 da suka hada da hadaddiyar daular Larabawa da Switzerland, sun shirya nune-nune da sunan kasashensu, da yawan nune-nunen da aka gudanar a taro, da sunan kasa ko hedkwatar kungiyar kasa da kasa. An samu karin zaman taruka 13 fiye da na baya, yayin da yawan ayyuka masu alaka da kasashen waje ya kai kaso 20.8 cikin 100, wanda ya shafi manyan kasashe da yakuna 27 cikin 30 dake kan gaba a fannin hidimar cinikayya, ta haka muna iya ganin yadda bikin baje kolin ya kara fadada rukunin abokan cinikayyar kasa da kasa。

Alkaluman da ma’aikatar masana’antu da fasahohin zamani ta kasar Sin ta gabatar sun nuna cewa, tsakanin watan Janairu da na Yulin bana, bangaren masana’antun samar da kayayyakin latironi masu alaka da fasahar sadarwa da na’urar kwamfuta na kasar na samun ci gaba cikin sauri, inda jimillar darajar karuwar manyan kamfanonin kera kayayyakin latironi ta karu da kashi 9.8%, idan an kwatanta da na bara.

A sa’i daya kuma, kamfanonin na kara fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen ketare, inda adadin ya karu da kashi 7.1%, bisa makamancin lokacin bara.

Sa’an nan a fannin samun kudin shiga, manyan kamfanonin kasar Sin masu kera kayan latironi, sun samu kudin da yawansa ya kai Yuan biliyan 8290.7, kwatankacin dalar Amurka biliyan 1199.5, tsakanin watan Janairu zuwa watan Yulin bana, adadin da ya karu da kashi 7.9%, bisa na makamancin lokacin bara.

Wadannan alkaluma sun nuna wani yanayi mai kyau, wajen raya bangaren masana’antun samar da kayayyakin latironi masu fasahohin zamani a kasar Sin. Bayanai na cewa, ya zuwa yanzu, yawan kamfanoni masu kera kayayyakin latironi, ya kai fiye da dubu 164 a kasar. Daga cikinsu, sabbin kamfanonin da aka kafa tsakanin watannin Janairu zuwa Yulin bana sun kai fiye da 9340. Hakan ya kara nuna yadda wadannan sassa za su taka rawa ga ci gaban tattalin arzikin Sin da ma duniya baki daya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)