logo

HAUSA

Najeriya ta lashi takwabin ganin bayan daukacin ayyukan ta’addanci nan da karshen bana

2022-09-07 10:33:25 CMG Hausa

Rahotannin da jaridar Daily Trust da ake wallawa a tarayyar Najeriya ta gabatar sun nuna cewa, ministan harkokin cikin gidan kasar Rauf Aregbesola, ya yi tsokaci yayin taron ganawa da manema labaran na hadin gwiwa da aka gudanar da ministocin tsaro da sadarwa da harkokin ‘yan sanda da hafsan hafsoshin rundunar sojojin tsaron kasar cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya, za ta ga bayan daukacin ‘yan ta’adda kafin watan Disamban bana.

Shi ma ministan tsaron kasar Bashir Magashi ya bayyana cewa, an yi nasarar murkushe sansanonin ‘yan ta’adda dake yankin arewa maso gabashin kasar, kuma sannu a hankali rayuwar jama’a da harkokin tattalin arziki a mafi yawan yankunan arewa maso gabashin kasar na farfadowa.

Amma masanin tsaro kuma jami’in shirin raya kasashe na MDD (UNDP) dake kasar, Mr Ume ya bayyana cewa, duk da cewa gwamnatin Najeriya tana kokari matuka domin daidaita matsalar, amma karuwar rashin daidaito da gibin arziki tsakanin al’umma, na iya kawo cikas ga shirin gwamnati na kawo karshen ta’addanci a karshen watan Disamba. (Jamila)