logo

HAUSA

MDD ta yi Allah-wadai da harin da ya hallaka fararen hula 35 a Burkina Faso

2022-09-07 10:17:47 CMG HAUSA

 

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ta bakin kakakinsa Stephane Dujarric, ya yi Allah wadai da harin bam din da aka kai a arewacin kasar Burkina Faso jiya Talata.

Sanarwar da hukumomin yankin suka fitar a daren ranar Litinin, ta bayyana cewa, wata babbar motar da ke cikin ayarin motocin da ke rakiya zuwa Ouagadougou, babban birnin kasar ce, ta taka nakiya, inda a kalla fararen hula 35 suka mutu, wasu 37 kuma suka jikkata.

Dujarric ya ce, sakatare janar din ya nanata kudurin majalisar, na ci gaba da yin aiki tare da Burkina Faso, da abokan huldar kasa da kasa don kare fararen hula, da magance kalubalen jin kai, da samar da dauwamammen zaman lafiya da wadata, da mutunta hakkin dan Adam. (Ibrahim Yaya)