logo

HAUSA

Al’ummar kasashen Turai na dandana kudar rikicin Rasha da Ukraine

2022-09-07 17:24:13 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei 

Yau kusan watanni shida ke nan, tun bayan barkewar rikici a tsakanin Rasha da Ukraine. Sakamakon rikicin, kamfanonin samar da makamai da na hatsi na Amurka sun ci kazamar riba, a yayin da kamfanonin samar da makamashi ma ba su so a bar su a baya.

Bayanai na nuna cewa, sakamakon yadda kasashen Turai suka biyewa kasar Amurka wajen kakaba takunkumai kan Rasha, yanzu haka, kasashen Turai da dama na fuskantar matsalar karancin makamashi mai muni, hakan ya tilasta musu sayen iskar gas daga wajen Amurka a kan farashi mai tsada, matakin da ya sa kamfanonin samar da makamashi na kasar Amurka cin kazamar riba, inda kusan kowane jirgin dakon iskar gas na kamfanonin Amurka da ke zuwa Turai, na iya cin kazamar ribar da ta kai dala miliyan 100.

Abin takaici shi ne, a yayin da ake fuskantar hauhawar farashin wutar lantarki da yadda aka kayyade wutar da ake samar musu, al’ummar kasashen Turai su ne suke dandana kudar rikicin. Kwanan nan ne, zanga zanga ta barke a birnin Prague, babban birnin kasar Czech, inda kimanin mutane dubu 70 suka bazama kan tituna suna kira ga gwamnati da ta dauki matakai na shawo kan saurin hauhawar farashin makamashi, tare da sukan gwamnati a kan manufarta ta yin biyayya ga kasashen yammaci wadda ta illata moriyar kasar.

Kwanan baya, shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya sake sanar da samar da gudummawar soji da za ta kai darajar kusan dala biliyan 3 ga kasar Ukraine. Kafin wannan, Amurkar ta samar da gudummawar soji a kalla dala biliyan 10.6 ga Ukraine. Kamar yadda tsohon dan majalisar dokokin kasar Burtaniya, George Galloway ya fada ne, “Kamar dai yadda Amurka ke son ganin Ukraine ta yi ta yaki har sai a karshe ta fadi kasa warwas, haka ta shirya ganin durkushewar Turai.”

Amurka dai ta tada rikicin tsakanin Rasha da Ukraine, ta kuma rika rura wutar rikicin, amma ta koma gyefe tana cin riba a fakaice. Nan ba da dadewa ba, za a shiga lokacin hunturu a Turai, amma ko kasashen Turai za su ci gaba da dandana kudar sakamakon rikicin? (Mai Zane:Mustapha Bulama)