logo

HAUSA

Mutane sama da miliyan 282 na fuskantar tsananin yunwa a yankin kudu da hamadar Sahara

2022-09-06 19:48:51 CMG Hausa

 

Hukumar kula da samar da abinci da raya aikin gona ta MDD (FAO), ta ce sama da mutane miliyan 282 ne ke fuskantar tsananin yunwa a yankin kudu da hamadar Sahara.

Jami’in hukumar mai kula da harkokin dazuka, Kenichi Shono, ya bayyana a yau, yayin jawabin bude taron kasa da kasa kan bishiyar Teak karo na 4 cewa, abubuwa da dama, ciki har da cutar COVID-19 da rikicin Rasha da Ukraine da matsalar yanayi ne suka haifar da tsanantar yanayin na baya-bayan nan.

Ya kara da cewa, baya ga yanayin yunwa, akwai kuma matsalar fari da ta addabi nahiyar.

A don haka, ya yi kira da a kara zuba jari wajen raya dazuka da shuka bishiyar Teak domin taimakawa shawo kan kalubalen da Afrika da ma duniya ke fuskanta. (Fa’iza Mustapha)