logo

HAUSA

Matashi dan kasar Chadi: Ci gaban China al’ajabi ne

2022-09-06 14:35:16 CMG Hausa

Kasar Sin ta bullo da shawarar “ziri daya da hanya daya” wato Belt and Road Initiative a shekara ta 2013. A wancan lokaci, wani matashi dan kasar Chadi mai suna Ahmat M. Issa, bai taba tsammanin shawarar za ta kawo manyan sauye-sauye haka ga kasarsa ba, kana, bai taba ganin cewa bayan wasu shekaru rayuwa da aikinsa za su yi alaka da shawarar ba.

Issa ya ce, lokacin da ya kuduri aniyar yin karatu a kasar Sin shekaru 10 da suka wuce, abokansa sun taba hana shi, inda ya ce:

“Sama da kaso 80 na abokan karatuna sun zabi karo ilimi a kasashen waje, kuma yawancinsu sun je kasashen Turai da Amurka, kadan daga cikinsu ne suka zabi kasashen Asiya, musamman kasar Sin. Amma ni a nawa ra’ayi, me zai hana in zo kasar Sin don koyon sabbin abubuwa?”

Issa ya ce, farkon zuwansa birnin Beijing na kasar Sin shekaru 10 da suka gabata, ya gano cewa, zabinsa ya yi daidai. Issa ya ce:

“Da na fita daga cikin babban filin saukar jiragen saman kasa da kasa a Beijing, na yi mamaki kwarai da gaske, ko na sauka a wani waje da ba Beijing ba ne? Wato abun da na yi tunani a baya da abun da na gani da idona, sun bambanta sosai. A baya ina ganin ko’ina akwai kekuna a Beijing. Amma ba haka ba ne.”

Issa ya ce ya taki sa’a har ya samu digiri na biyu a fannin karatu, da nakaltar harshen Sinanci sosai. Issa ya samu wani suna na harshen Sinanci da ake kira Zhang Xiaoqiang, wanda a yanzu haka yake jin dadin rayuwa da aiki sosai a kasar Sin. Yanzu akwai ‘yan kasar Chadi da dama wadanda suka nemi Issa ya musu karin bayani kan yiwuwar yin karatu a kasar Sin.

Issa ko kuma Zhang Xiaoqiang ya ce:

“Ina ganin kamar tun daga shekara ta 2016 ko kuma 2015, an kara samun mutanen da suke son yin karatu a kasar Sin, kana mutane sun kara fahimtar kasar, da bayyana sha’awarsu ta zuwa kasar.”

A ganin malam Issa, babban dalilin da ya kawo wannan canji shi ne aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, inda mutanen kasar Chadi dake tsakiyar nahiyar Afirka suka kara fahimtar halin da ake ciki a kasar Sin, al’amarin da ya kyautata rayuwar mutanen Afirka kwarai da gaske. Issa ya ce:

“Na gano wasu manyan sauye-sauyen da suka wakana a kasata Chadi. Tun bayan da kasar Sin ta bullo da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ a shekara ta 2013, har zuwa yanzu, kamfanonin kasar Sin da yawa sun shiga nahiyar Afirka, ciki har da kamfanonin kasar Sin da suke gudanar da aikin inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma a Chadi, don haka da na koma gida, na gano manyan sauye-sauye. A cikin shekaru 10, na ganewa idanuna manyan nasarorin hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka, kuma a zahiri suke.”

Alkaluman sun nuna cewa, zuwa karshen shekara ta 2021, daga cikin kasashen Afirka 53 da suka kulla alakar jakadanci da kasar Sin, akwai guda 52 gami da kungiyar tarayyar Afirka, wadanda suka rattaba hannu tare da kasar Sin kan yarjejeniyar hadin-gwiwa kan aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” tare.

A ganin malam Issa, akwai dalilai da dama da suka sa kasashen Afirka ke sha’awar shiga shawarar “ziri daya da hana daya”. Na farko, a karkashin tsarin dandalin FOCAC, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, nasarorin hadin-gwiwar Sin da Afirka sun kara bayyana, na biyu kuma shi ne, kasashen Afirka suna son koyon dabarun kasar Sin a fannin samar da ci gaba.

Malam Issa ya ce:

“Shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ ta kara hadin-gwiwa da dankon zumunta tsakanin Sin da Afirka, kuma kasashen Afirka da dama sun kalli shawarar a matsayin mai kyau. Ina ganin za’a kara samar da abubuwan al’ajabi karkashin shawarar a nan gaba, saboda ci gaban kasar Sin abun al’ajabi ne, a sabili da haka, kasashe da dama suna matukar son koyon dabarun kasar Sin na neman ci gaba, musamman ta hanyar aiwatar da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’.”

Har wa yau, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta haifar da damammaki ga ayyukan malam Issa. A yayin da yake karatun digiri na farko a kasar, shi da abokan karatunsa sun gwada wasu sana’o’in da suka shafi cinikayyar Afirka da Sin, har sun bude wani kamfani. A nasa ra’ayi, kasar Sin na da manyan kasuwanni gami da damammaki daban daban, inda ya ce:

“Kasar Sin na da yanayi mai kyau wajen raya sana’o’i daban-daban. Tana da jama’a da yawansu ya zarce biliyan 1, da babbar kasuwa, kana, mutanen kasar na da kwazon aiki. A nan, ba za’a samu wani dalili na yin kasala ba.”

Sakamakon kokarinsa na raya sana’o’i, Issa ya fara sanin kungiyar bunkasa sana’o’in da suka shafi shawarar “ziri daya da hanya daya” ta Zhongguancun dake Beijing, ko kuma ZBRA a takaice, wadda ta kaddamar da wani aikin yin kirkire-kirkire da raya sana’o’i don taimakawa daliban kasashen waje dake kasar Sin a shekara ta 2017, har ma shi kansa ya fara aiki a wannan kungiya a shekara ta 2019, inda yake himmatuwa wajen samar da ci gaba ga hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin tattalin arziki da kasuwanci.

Malam Issa ya bayyana nasa fahimta game da hadin-gwiwar Sin da Afirka, inda ya ce:

“A shekara ta 2018, na fara samun fahimta kan menene ainihin hadin-gwiwar Sin da Afirka. Musamman taron koli na Beijing na dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka a shekarar, ya sa na fahimci cewa, akwai abubuwa da yawa da zan iya yi domin karfafa hadin-gwiwar bangarorin biyu.”

A ’yan shekarun nan, sakamakon muhimman bukukuwa da dama, ciki har da bikin baje-kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE, da bikin baje-kolin tattalin arziki da kasuwanci na Sin da Afirka, da bikin sayen kyawawan kayayyakin Afirka ta kafar intanet, akwai ire-iren amfanin gonan kasashen Afirka da suka shigo kasuwannin kasar Sin, ciki har da lemu daga Afirka ta Kudu, da kofi daga Habasha, da kayan teku daga Namibiya. A wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC wanda aka yi a watan Nuwamban bara, kasar Sin ta sanar da daukar matakan kawo sauki ga harkokin shigar da amfanin gona na kasashen Afirka cikin kasar. A farkon watan Agustan bana kuma, karo na farko kasar Kenya ta fara fitar da avocadonta zuwa kasar Sin, al’amarin da ya shaida mu’amalar ciniki mai karfi tsakanin Sin da Kenya, da ma kasashen Afirka baki daya.

Issa ya ce, kasar Sin tana son shigar da amfanin gona mai inganci daga kasashen Afirka, kuma Afirka na da abubuwa da yawa da kasar Sin take bukata. Shigar da hajojin Afirka masu kyau cikin kasar Sin, yana samar da zarafi mai kyau ga manoman Afirka da mutanen Afirka dake kokarin bunkasa sana’o’i a kasar Sin.

Issa ya ce, yana fatan ci gaba da kokari don amfani da babban zarafi na ingantar hadin-gwiwar Afirka da Sin, don kara raya sana’o’insa, ta yadda zai bada karin gudummawa ga sada zumunta tsakanin bangarorin biyu. (Murtala Zhang)