logo

HAUSA

Odinga ya ce yana mutunta hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke kan zaben shugaban kasar

2022-09-06 10:54:55 CMG Hausa

Shugaban 'yan adawar kasar Kenya Raila Odinga, kana babban mai shigar da kara a gaban kotu yana kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar Kenya na 2022, ya ce, yana mutunta hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke jiya Litinin, inda ta tabbatar da nasarar da William Ruto ya samu a zaben, duk da cewa, bai amince da sakamakon zaben ba.

A wani takaitaccen hukunci da aka yanke a birnin Nairobi, alkalan kotun kolin baki daya, sun yi watsi da korafe-korafen da ya gabatar, saboda rashin cancanta da gaza gabatar da kwararan shaidu.

Koda ya ke, Odinga ya ce lauyoyinsu sun gabatarwa kotun hujjojin da ba za su iya karyatawa ba, kuma hujjojin gaskiya ne, amma abin takaici alkalan sun kawar da kai.

A ranar 15 ga watan Agusta ne, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Kenya ( IEBC) ta ayyana William Ruto mai shekaru 56, a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar, bayan da ya samu kuri’u miliyan 7.17 ko kashi 50.49 cikin 100 na kuri’u miliyan 14.1 da aka kada.

A cewar alkaluman hukumar zaben, Odinga yana biye da Ruto a zaben shugaban kasar da ya samu halartar ’yan takara 4, inda ya samu kuri’u miliyan 6.94 ko kashi 48.85 na kuri’u miliyan 14.1 da aka kada. (Ibrahim)