logo

HAUSA

Mamakon ruwan sama ya hallaka mutane 3 a Senegal

2022-09-05 11:04:50 CMG Hausa

Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya bayyana alhinin rasuwar mutane 3, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka fara a sassan kasar daban daban, ciki har da birnin Dakar tun daga ranar Asabar.

Shugaba Sall, ya ce mamakon ruwan saman ya sabbaba rasuwar mutane 2 a Camberene da Yeumbeul dake wajen birnin Dakar, da kuma wani mutum guda a Sadel na arewacin kasar. Ya ce an samu ruwan sama mai matukar yawa a dan lokaci kankani, kuma Senegal na fuskantar wani mawuyacin lokaci na hasashen yanayin da ka iya aukuwa.

Sai dai duk da hakan, shugaba Sall ya ce ya umarni ministan ma’aikatar cikin gida, ruwa da tsaftar muhalli, da na ma’aikatar hadin kan kasa, da su aiwatar da matakan tallafawa al’ummun da ibtila’in ya shafa. (Saminu Alhassan)