logo

HAUSA

Gwano Ba Ya Jin Warin Jikinsa

2022-09-05 21:20:23 CMG Hausa

Waye mai satar shiga yanar gizo mafi muni a duniya? Yau Litinin hukumar daidaita mummunar manhajar da ta bata kamfuta ta kasar Sin da kuma kamfanin Qihoo 360 na kasar Sin, suka gabatar da rahotannin binciken batun kutsen yanar gizo da aka yi wa jami’ar koyon ilmin masana’antu ta yankin arewa maso yammacin kasar Sin wato NPU. Wani abun shaida ne na daban.

Rahotannin sun nuna cewa, ofishin kula da aikin kai harin musamman wato TAO dake karkashin jagorancin hukumar kula da tsaron kasar Amurka wato NSA, ya yi amfani da hanyoyi 41 wajen yi wa yanar gizon NPU kutse fiye da sau dubu 1 da kuma satar bayanan wasu muhimman fasaha. Ban da haka kuma, a shekaru da dama da suka wuce, ofishin TAO ya yi kutsen yanar gizo kan wasu kamfanoni jagororin sana’o’in kasar Sin, hukumomin kasar, jami’o’i da hukumomin lafiya da nazarin kimiyya, inda ya sarrafa na’urorin yanar gizo masu ruwa da tsaki, kuma ana ganin cewa, ya saci wasu bayanai masu daraja.

Rahotannin sun gabatar da cikakkun shaidu, wadanda suka shafi mutane 13 a Amurka wadanda suka yi kutsen kai tsaye, akwai kwangiloli fiye da 60 da takardu fiye da 170 a tsakanin ofishin TAO da ‘yan kasuwan sadarwa na Amurka dangane da samar da yanayin yin kutsen. Wadannan shaidu sun nuna wa duniya yadda NSA ba tare da jin kunya, ta aikata wannan mugun abu a yanar gizo, sun kuma tabbatar da yadda gwamnatin Amurka ke satar bayanai a yanar gizo, amma ta yi shelar cewa, ana yi mata kutsen yanar gizo.

Rahotannin bincike da kasar Sin ta gabatar sun nuna aniyar kasar Sin wajen yaki da satar bayanai a yanar gizo da kuma tsaron kanta yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)