logo

HAUSA

’Yan bindiga sun yi garkuwa da gwamman matafiya a hanyar Benin zuwa Owo a kudancin Najeriya

2022-09-05 10:31:00 CMG HAUSA

 

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa, wasu gungun ’yan bindiga sun yi awon gaba da gwamman fasinjoji, dake cikin wasu motoci kirar Bas 2, a wani daji dake kusa da garin Ifon, a kan hanyar Benin zuwa Owo na jihar Ondo.

Da take tabbatar da aukuwar lamarin a jiya Lahadi, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ondo Funmilayo Ibukun Odunlami, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ’yan bindigar sun tare matafiyan ne da yammacin ranar Asabar, lokacin da suke dawowa daga bikin binne gawa a jihar Edo dake makwaftaka da Ondo.

Odunlami ta ce jim kadan da aukuwar lamarin, ’yan sanda sun bazama domin ceto wadanda aka yi garkuwan da su, sun kuma yi nasarar kwato wani adadi na matafiyan a jiya Lahadi, ko da yake ta ce ba a kai ga tantance ainihin adadin wadanda aka ceto din ba.

Jami’ar ta kara da cewa, babu cikakkun alkaluman adadin wadanda ’yan bindigar suka yi garkuwa da su, amma dai ’yan sanda na ci gaba da aiki tukuru domin ceto su baki daya. To sai dai kuma wasu majiyoyin yankin da lamarin ya auku, sun ce matafiyan da aka sace sun kai mutum 32.

(Saminu Alhassan)