logo

HAUSA

AU ta lashi takobin samar da tsaro duk da karuwar hare-haren al-Shabab a Somalia

2022-09-04 15:40:14 CMG Hausa

 

Rundunar wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afrika a kasar Somalia (ATMIS), ta lashi takobin hada hannu da rundunonin tsaron kasar, domin wanzar da tsaro duk da karuwar hare-haren kungiyar al-Shabab a kasar.

Rundunar ATMIS ta yi tir da harin da mayakan kungiyar al-Shabab suka kai a ranar Juma’a da dare kan jerin gwanon motocin ‘yan kasuwa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 20, tare da lalata motocin daukar kaya 7, dake dauke da kayayyakin abinci da ruwa da ake bukata a garin Hiran na yankin tsakiyar kasar.

Wata sanarwar da runduanr ATMIS ta fitar jiya a Mogadishu, babban birnin kasar, ta jajantawa iyalan wadanda suka rasu, tare da bayyana kudurin ATMIS din na ci gaba da hada hannu da dakarun gwamnatin Somalia wajen wanzar da tsaro da zaman lafiya a kasar.

Mazauna sun bayyana cewa, harin na baya-bayan nan, na ramuwar gayya ce kan wata kungiyar ‘yan banga ta Ma'awisley wadda ke samun goyon bayan rundunar sojin Somalia, wadda kuma a baya bayan nan ke yakar mayakan al-Shabab da zummar fatattakarsu daga yankin Hiran. (Fa’iza Mustapha)