logo

HAUSA

An fara yi wa masu kada kuri’a rajista gabanin babban zaben kasar Saliyo

2022-09-04 15:30:29 CMG Hausa

 

Hukumar zabe ta kasar Saliyo (ECSL), ta fara yi wa masu kada kuri’a rajista a jiya Asabar, domin shiryawa babban zaben kasar da za a yi a badi.

Shugaban hukumar Mohamed Konneh, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, aikin rajistar zai gudana ne bisa matakai biyu, wadanda kuma kowanne zai dauki tsawon kwanaki 15, yana mai cewa, an kafa sama da cibiyoyin rajista 2,000 a fadin kasar.

Ya kara da cewa, hukumar za ta hada hannu da hukumomin tsaro domin tabbatar da al’ummar kasar sun samu damar isa cibiyoyin tare da yin rajista ba tare da wani tsaiko ba.

Ya ci gaba da cewa, suna son tabbatar da ‘yancinsu a shekarar 2023 kuma hanya daya tilo ta yin hakan ita ce rajistar zabe. Ya ce za su iya sauya matsin tattalin arziki da ake fuskanta ne ta hanyar rajista kadai.

An shirya gudanar da babban zabe a kasar Saliyo ne a ranar 24 ga watan Yunin shekarar 2023. (Fa’iza Mustapha)