logo

HAUSA

UNICEF: yawan kananan yara da aka raba su da muhallansu ya kafa tarihi tun bayan babban yakin duniya na 2

2022-09-04 16:38:17 CMG Hausa

 

Sabbin alkaluman da asusun kula da kananan yara na MDD wato UNICEF ya gabatar a kwanan baya ya nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2021, yawan kananan yara da hargitsi, tada tsaune tsaye da sauran rikice-rikice suka raba su da muhallansu a sassa daban daban na duniya ya kai miliyan 36 da dubu 500, wanda ya kafa tarihi tun bayan babban yakin duniya na 2.

Asusun UNICEF ya yi nuni da cewa, wadannan kananan yara sun hada da ‘yan gudun hijira da wadanda suka nemi mafaka miliyan 13 da dubu 700, da wasu kusan miliyan 22 da dubu 800 wadanda suka bar gidajensu sakamakon hargitsi da tada tsaune tsaye a cikin gida. Wannan adadi bai hada da wadanda suka bar gidajensu sakamakon matsalar sauyin yanayi, muhalli da bala’i daga indallahi ba.

Asusun ya kara da cewa, adadin ya biyo bayan jerin matsaloli da dama, ciki hadda mummunan hargitsin da yake ci gaba da faruwa a kasar Afghanistan, da tashin hankali a kasar Congon(Kinshasa) da Yemen, wadanda suka ci gaba karuwa sakamakon illolin sauyin yanayi.

Asusun na UNICEF ya yi fatan cewa, irin wannan adadi wanda ya girgiza mutane matuka, zai karfafa gwiwar gwamnatocin kasa da kasa, da su dauki matakai na kare kananan yara daga barin gidajensu, da kuma tabbatar da ba su hidimomin ilmi, kariya da sauran hidimomin da suka wajaba.

Har ila yau, asusun ya yi bayanin cewa, a cikin kananan yara dake gudun hijira, rabinsu ne kawai suka samu damar zuwa makarantar firamare. Sa’an nan kuma, matasa ‘yan gudun hijira da yawansu bai wuce rubu’i ba sun samu damar shiga makarantar midil. Yawan kananan yara da aka raba su da muhallansu da kuma ‘yan gudun hijira wadanda suke bukatar magani, ilmi, da kariya ya kafa tarihi. Baya ga haka kuma, kananan yara wadanda ba su da masu yi musu rakiya ko kuma an raba su da iyalansu, suna fuskantar babbar barazanar yin fataucinsu, cin zarafinsu, nuna musu karfin tuwo da muzguna musu. A duk fadin duniya kuma, yawan kananan yara ya kai kashi 28 cikin kashi dari na jimillar wadanda aka yi fataucinsu. (Tasallah Yuan)